Bayan watanni 11, Iyalan yan kasuwa canjin Kano da DSS ta kama sun ga mazajensu

Bayan watanni 11, Iyalan yan kasuwa canjin Kano da DSS ta kama sun ga mazajensu

  • Mata, yara da iyayen mutum 45 da gwamnatin tarayya ta damke a jihar Kano sun samu daman ganin mazajensu
  • Kimanin shekara daya yanzu, an damke yan kasuwan canjin da ake zargin sun taimaka wajen turawa yan Boko Haram kudi
  • Ministan Labarai a bayyana cewa za'a gurfanar da su a kotu nan ba da dadewa ba

Kano - Bayan kimanin shekara guda tsare hannu hukumar DSS a Abuja, an baiwa yan kasuwan canjina jihar Kano 45 da akewa zargin ta'addanci daman ganin iyalansu.

Daily Trust ta ruwaito cewa a ranar Talata, Habiba Ibrahim Ladan, daya daga cikin matan mazajen ta bayyana cewa suna da zuwa Abuja ganin mazajensu da yaransu.

Tace suna godiya da Antoni Janar na tarayya, Abubakar Malami, da gwamnatin tarayya da suka basu damar ganinsu.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Gwamnonin APC sun shiga ganawar gaggawa da Shugaba Buhari

Bayan watanni 11
Bayan watanni 11, Iyalan yan kasuwa canjin Kano da DSS ta kama sun ga mazajensu Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Hakazalika Halima Garo, wacce tuni ta shiga Abuja kuma ya koma Kano, ta tabbatar da cewa ta ga mijinta.

Tace:

"Duk suna nan da rai cikin koshin lafiya; mun gode Allah. Kawai dai hankulansu ya tashi kuma sun rame, amma mun godewa Allah."

An tattaro cewa za'a gurfanar dasu fari daga gobe 23 ga Febrairu, ranar 28 ga Febrairu, 1 ga Maris da 8 ga Afrilu.

Iyalan yan BDC da ake zargi da turawa yan Boko Haram kudi a Kano sun yi kuka

Iyalan yan kasuwar canji 45 a jihar Kano da aka damke watanni 11 da suka gabata sun yi kira ga gwamnati ta sakin musu mazajensu ko kuma ta gurfanar da su a kotu.

Kara karanta wannan

An gurfanar da mata 3 kan laifin jika AlKur'ani da jinin biki da jefawa cikin masai a Zamfara

Iyalan wanda suka hada da mata da yara sun kai kuka fadar mai martaba sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, ranar Alhamis, 4 ga watan Febrairu, 2022, rahoton Daily Trust.

Sun bayyana cewa rashin mazajensu da iyayen yaransu ya jefasu cikin mumunan hali.

Bayan sauraron korafinsu, Sarkin Kano ya bukaci mutum biyar cikin matan su rubuta korafinsu a takarda kuma yayi alkawarin daukan mataki.

Zaku tuna cewa an damke wani yan kasuwan canji da zargin taimakawa wajen turawa yan ta'addan Boko Haram kudi.

Daga cikin yan kasuwan canji 45 da aka damke akwai Baba Usaini, Abubakar Yellow (Amfani), Yusuf Ali Yusuf (Babangida), Ibrahim Shani, Auwal Fagge da Muhammad Lawan Sani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel