Yakin Iran: Matsala Ta Tunkaro Gwamnatin Trump, an Shirya Tsige Mukarrabansa
- Wani ɗan majalisar dokokin Amurka ya ce zai sake gabatar da ƙudirin tsige Ministan Tsaro Pete Hegseth mako mai zuwa
- Yunkurin tsige ministan ya ƙara ƙarfi bayan yaƙin Iran da ya goyi baya ya taimaka wajen rasa ikon Majalisa da jam’iyyar Republican
- Donald Trump ya kare Hegseth, yana mai cewa ya yi aiki mai kyau, yayin da wasu ’yan majalisa ke neman a sauke shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Wasu ’yan majalisar dokokin Amurka na shirin sake yunƙurin tsige Ministan Tsaro, Pete Hegseth.
Wannan na zuwa ne bayan zaben yan majalisa, an shirya hakan ne mako mai zuwa, yayin da matsin lamba kan mukaminsa ke ƙaruwa.

Source: UGC
Yunkurin ya samu ƙarin ƙarfi ne bayan yaƙin Iran da Hegseth ya goyi baya, wanda a wani ɓangare ya taimaka wa jam’iyyar Republican rasa ikon Majalisa a zaɓen tsakiyar wa’adi, cewar CBS News.
Ɗan majalisa zai gabatar da ƙudirin tsige Hegseth
Thomas Massie, ɗan majalisa mai wakiltar Kentucky a jam’iyyar Republican, ya shaida wa Bloomberg News cewa babu shakka zai sake gabatar da ƙudirin tsige Hegseth idan Majalisa ta koma zama mako mai zuwa.
Wannan dai ba shi ne karon farko da Massie ya nemi a tsige ministan ba. A baya ya gabatar da irin wannan ƙudiri bisa zargin cewa Hegseth ya jagoranci yaƙin Iran ba tare da amincewar Majalisa ba.
A halin yanzu, ana ta hasashen cewa ministan na iya rasa kujerarsa sakamakon rikicin siyasar da ya dabaibaye shi.

Source: Getty Images
Trump ya kare ministan tsaro
A ranar Alhamis, Shugaba Donald Trump ya bayyana wa manema labarai cewa Hegseth ya yi aiki mai kyau matuƙa.
Trump ya ce ministan na iya fuskantar adawa ne saboda matakan da ya ɗauka na rage wasu shirye-shiryen bambancin jinsi da haɗa kan al'umma a Ma'aikatar Tsaro.

Kara karanta wannan
An fara batun Tinubu ya je Umrah ne don neman kuri'un 'yan Arewa, hadiminsa ya magantu
Shi ma Hegseth ya wallafa wani bidiyo na tsawon mintuna shida a shafinsa na X, inda ya kare aikinsa a matsayin minista.
A cikin bidiyon, ya bayyana Massie a matsayin ɗan majalisa mai takaici da ya sha kaye, tare da zargin cewa ƙudirin tsige shi da ya gabatar ba shi da tushe.
Massie ya bukaci Trump ya kori Hegseth
Massie, wanda ya sha kaye a zaɓen fitar da gwani bayan Trump ya goyi bayan wani ɗan takara a kansa, ya bukaci shugaban ƙasar ya kori Pete Hegseth cikin gaggawa.
Ya ce hakan zai bai wa Majalisar Dattawa damar tabbatar da sabon ministan kafin jam’iyyar Democrat ta karɓi iko da Majalisa a watan Janairu.
A wani saƙo da ya wallafa a kafafen sada zumunta, Massie ya ce ƙudirin da yake son gabatarwa bai kai tsananin matakan da 'yan Democrat za su ɗauka ba idan suka karɓi ikon Majalisa.
Ya yi hasashen cewa 'yan Democrat za su gudanar da zaman sauraron bayanai da kuma shari'o'i kan ministan.
Vance ya magantu kan faduwarsu zabe
Mun ba ku labarin cewa JD Vance ya ce yawancin magoya bayan Donald Trump da suka zaɓi tikitin Trump-Vance a 2024 sun koma zaɓen ’yan Democrat a 2026.
Yaƙin Iran, tsadar rayuwa, hauhawar farashi da manufofin ƙasashen waje na Amurka na daga cikin dalilan da suka sa masu zaɓe suka juya wa Republican baya.
Vance ya ce masu zaɓen da suka sauya sheƙa sun buƙaci a kawo ƙarshen yaƙin, a fifita Amurka da kuma sauya dangantakarta da Isra’ila.
Asali: Legit.ng

