Gawuna Ya Ajiye wa Tinubu Mukaminsa ana Zargin Yana Shirin Hade wa da Kwankwaso

Gawuna Ya Ajiye wa Tinubu Mukaminsa ana Zargin Yana Shirin Hade wa da Kwankwaso

  • Tsohon 'dan takarar gwamnan Kano, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya yi murabus daga shugabancin kwamitin FMBN
  • Gawuna ya bayyana cewa ajiye aikinsa ya biyo bayan umarnin shugaban ƙasa domin bin dokar zaɓen Najeriya
  • Ana sa ran Dr. Nasiru Yusuf Gawuna zai koma jam’iyyar ADC tare da jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Tsohon ɗan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna, ya yi murabus daga mukaminsa na shugaban kwamitin gudanarwa na Bankin Lamunin Gidaje na Ƙasa (FMBN).

Rahotanni sun nuna cewa Gawuna ya kammala shirin sauya sheƙa zuwa jam’iyyar ADC tare da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.

Gawuna ya yi murabus daga mukamin FMBN
Tsohon mataimakin gwamnan Kano Nasiru Yusuf Gawuna, Shugaban Kasa Bola Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Jaridar Daily Nigerian ta wallafa cewa ana sa ran zai sanar da sabon matakin nasa a hukumance nan ba da jimawa ba.

Kara karanta wannan

"Allah na fushi da Kwankwaso," NNPP ta fadi dalilin rikicin da ya taso a ADC

Nasiru Yusuf Gawuna ya yi murabus

Jaridar Leadership ta wallafa cewa Nasiru Gawuna ya sanar da yin murabus a wasiƙa mai ɗauke da kwanan wata 27 ga Maris, 2026.

Gawuna ya bayyana cewa murabus ɗin nasa ya fara aiki nan take, yana mai cewa matakin ya yi daidai da umarnin shugaban ƙasa na masu neman mukamai su yi murabus kafin ya nemi kujerar zabe.

Ya bayyana cewa ya ɗauki matakin ne bisa umarnin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, wanda ya umarci duk masu rike da mukaman siyasa da su sauka domin bin tanadin dokar zaɓe.

Ana tsoron Gawuna zai hade da Kwankwaso
Nasiru Yusuf Gawuna tare da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

A cewarsa:

“Murabus na ya zo ne bisa cikakken bin umarnin shugaban ƙasa wanda ya buƙaci duk masu mukaman siyasa su sauka bisa tanadin dokar zaɓe.”

Ya ƙara da cewa bin wannan umarni na da muhimmanci wajen tabbatar da gaskiya da adalci a harkokin siyasa, musamman a daidai lokacin da ake shirin wasu manyan ayyuka na siyasa a ƙasar.

Kara karanta wannan

Tafiyar Gawuna ADC ta fara lahanta APC a Kano, shugaba a jam'iyya ya bi ubangidansa

Gawuna ya gode wa Tinubu

Gawuna ya nuna matuƙar godiyarsa ga shugaban ƙasa bisa damar da aka ba shi na yin hidima, yana mai cewa wannan dama ta ba shi ƙwarewa da damar bayar da gudunmawa ga ci gaban bankin da kuma ƙasar baki ɗaya. Ya ce:

“Ina matuƙar godiya ga shugaban ƙasa bisa wannan dama da ya ba ni na yin hidima, wanda na ɗauka a matsayin wata babbar gata.”

Gawuna ya bayyana cewa ya miƙa makomarsa gaba ɗaya ga Allah (SWT), yana neman shiriya kan matakin da zai ɗauka na gaba a rayuwarsa ta siyasa. Haka kuma, ya tabbatar da cewa zai mika ragamar aiki cikin lumana da bin ƙa’idojin da aka shimfiɗa, domin tabbatar da cewa babu wata tangarda a harkokin bankin bayan ficewarsa.

Ba za mu zaɓi Tinubu ba – Ɗan gwagwarmaya

Mamman Buhari, ɗaya ne daga cikin matasa da ke gwagwarmayar siyasa a Kano, ya kuma yi magana da Legit game da guguwar siyasa a jihar.

Kara karanta wannan

Jagora a APC, Danbilki Kwamanda ya fadi wanda zai ci zaben Kano a 2027

Ya bayyana cewa:

"Mu ba za mu zaɓi Bola Tinubu KO APC na, ko gwamna Abba Kabir Yusuf na za mu zaba a Kano ba."

Ya ce duk da a baya bai cika goyon bayan Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ba, amma a wannan karon za su bi duk wanda suke da tabbacin zai yi masu aiki.

An kasa samun Gawuna a waya

A baya, mun wallafa cewa tsohon dan takarar Gwamnan jihar Kano, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya fara tayar wa da hankalin jam'iyya mai mulki ta APC.

Rahotanni 'yan kwanakin nan sun fara nuna yadda Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da Nasiru Yusuf Gawuna ke 'dasawa sosai, har ake tsammanin zai sauya sheka.

Sai dai an samu labarin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya shiga damuwa, ya fara neman hana 'kara karfin alaka a tsakanin Kwankwaso da Gawuna.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng