'Ba da Yawun Mu ba," Birtaniya Ta Kware wa Shugaba Trump baya a Yaki da Iran
- Gwamnatin Burtaniya ta musanta ikirarin Isra'ila cewa Iran tana da makaman da za su iya kai wa kasashen Turai hari a yau Lahadi
- Minista Steve Reed ya bayyana cewa kalaman Donald Trump na ruguza matatun man Iran na kashin kansa ne, ba na kasar Burtaniya ba
- Burtaniya ta lashi takobin guje wa shiga yakin Iran, inda ta zabi yin aiki da kawayenta domin kwantar da tarzomar yankin
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Birtaniya - Ministan majalisar zartarwar Birtaniya, Steve Reed, ya bayyana cewa babu wani bincike da ya tabbatar da ikirarin cewa Iran na shirin kai wa Turai hari da makamai masu linzami.
Ya kara da cewa ba su da masaniyar ko ma Iran din tana da karfin kai hari zuwa kasashen Turai a halin yanzu.

Kara karanta wannan
Makamin da Iran ta harba ya keta tsaron Isra'ila, ya fada kusa da cibiyar nukiliya

Source: Getty Images
Birtaniya ta musanta ikirarin Isra'ila kan Iran
Wannan raddi ya biyo bayan wani sako ne da rundunar sojin Isra'ila (IDF) ta wallafa a kafofin sada zumunta ranar Asabar, inda ta ce Iran na da makaman da za su iya dakar biranen London, Paris, ko Berlin, in ji rahoton Reuters.
A wata hira da kafar watsa labaran BBC, Steve Reed wanda shi ne ministan gidaje na Birtaniya, ya ce babu wani rahoton sirri da ya goyi bayan wadannan kalaman na Isra'ila.
"Ba ni da masaniyar cewa ma Iran din na nufin farmakar Turai, ballantana a kai ga maganar ko tana da ikon yin hakan idan ma ta yi yunkurin."
- Steve Reed.
Matsayar Birtaniya kan barazanar Trump
Yayin da yake magana da manema labarai, Reed ya bayyana cewa kalaman Shugaba Trump na "shafe" matatun makamashin Iran na kashin kansa ne.
Trump dai ya bai wa Tehran wa'adin sa'o'i 48 ta sake bude mashigar ruwan Hormuz baki daya, idan kuma ba haka ba zai yi mata barna mai tsanani, in ji rahoton Reuters.

Kara karanta wannan
Isra'ila ta jawo wa kanta, Rasha ta shiga kafar wando daya da ita kan hari a Lebanon
Da aka tambaye shi matsayar Burtaniya kan wannan wa'adi na Trump, Reed ya ce shugaban Amurka na da ikon kare kalaman kansa, amma dai bai yi magana da yawunsu ba.

Source: Getty Images
Birtaniya ba za ta shiga yaƙin Iran ba
Ministan ya fayyace cewa Burtaniya ba za ta bari a ja ta cikin wannan yaki ba, amma za ta kare nata muradun a yankin Gabas Ta Tsakiya.
Ya kara da cewa kasarsa za ta ci gaba da aiki tare da kawayenta domin kwantar da tarzomar da ake ciki maimakon rura wutar yaki.
Wannan mataki na Burtaniya na nuna alamun rarrabuwar kai tsakanin Amurka da manyan kawayenta na Turai game da rikicin na Iran.
Hormuz: Iran ta gargadi kawayen Amurka
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kasar Iran ta yi martani ga kasashe a duniya bayan barazanar Amurka game da rufe mashigar Hormuz da aka yi.
Iran ta ce mashigan Hormuz a bude yake ga jiragen ruwa, sai dai wadanda ke da alaka da abokan gabanta, yayin da rikici ke kara tsananta.
Jami’in Iran Ali Mousavi ya bayyana cewa jiragen da ba na makiya ba za su iya wucewa idan sun hada kai da Tehran wajen tsaro da aminci.
Asali: Legit.ng