BRICS Ka Iya Shiga Tsakani, an Ji Tattaunawar Shugaban Iran, Firayim Ministan India

BRICS Ka Iya Shiga Tsakani, an Ji Tattaunawar Shugaban Iran, Firayim Ministan India

  • Shugaban Iran ya bukaci ƙungiyar kasashen BRICS ta taka rawar gani wajen dakatar da rikicin Gabas ta Tsakiya
  • Ya zargi Amurka da Isra’ila da kai hare-hare ba tare da hujja ba, ya ce Iran ba ita ta fara rikicin ba kuma tana son a dakatar da yaƙi
  • Firaministan India ya nuna damuwa kan rikicin, ya bukaci a kiyaye tsaron hanyoyin ruwa kamar mashigan Hormuz

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tehran, Iran - Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi wata tattaunawa da Firayim ministan India, Narendra Modi.

Pezeshkian ya bukaci ƙungiyar BRICS ta zama mai zaman kanta wurin taka rawar gani wajen kawo ƙarshen rikicin da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya.

Shugaban Iran ya yi magana da Firayim ministan India
Shugaba Masoud Pezeshkian na kasar Iran da ake ci gaba da yaki. Hoto: Iran Military Media.
Source: Getty Images

Shugaban Iran ya tattauna da Narendra Modi

Ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da Firaministan India, Narendra Modi, cewar Tribune India.

Kara karanta wannan

Ana cikin yaki da Amurka, Isra'ila, shugaban Iran ya samo mafita ga kasashen Musulmi

Pezeshkian ya jaddada muhimmancin dakatar da faɗa da kuma tabbatar da zaman lafiya a duniya.

Pezeshkian ya bukaci ƙasashen BRICS su taimaka wajen rage tashin hankali, musamman ganin cewa India ce ke jagorantar ƙungiyar a wannan shekara, yana mai kira ga haɗin kai.

Ya kuma yi bayanin halin da yankin ke ciki, tare da nanata cewa dole ne a kawo ƙarshen rikici tare da hana ci gaba da yaɗuwar tashin hankali.

Shugaban Iran ya kuma gabatar da shawarar kafa tsarin tsaro na yankin Gabas ta Tsakiya wanda ƙasashen yankin za su jagoranta ba tare da tsoma bakin ƙasashen waje ba.

A cewarsa, dakatar da hare-haren da Amurka da Isra’ila ke kaiwa Iran shi ne matakin farko na kawo ƙarshen rikicin, tare da tabbatar da cewa ba za su sake faruwa ba.

Pezeshkian ya bukaci hadin kan kasashen BRICS
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian da Firayim ministan India, Narendra Modi. Hoto: Anadolu Ajansi, Biju BORO/AFP.
Source: Getty Images

Zargin da Iran ke yi wa Amurka

Pezeshkian ya zargi Amurka da Isra’ila da aikata hare-hare ba bisa ka’ida ba, yana mai cewa an kai farmaki Iran yayin tattaunawar nukiliya ba tare da hujja ba.

Kara karanta wannan

Ta fasu: Shirin da Trump yake yi don matsawa Iran lamba ta saduda kan Hormuz

Ya ce hare-haren sun yi sanadin mutuwar manyan jami’ai da fararen hula ciki har da yara makaranta, tare da lalata muhimman kayayyakin more rayuwa.

Haka kuma ya yi ikirarin cewa Amurka ta kai hari makaranta a Minab wanda ya yi sanadin mutuwar yara 168 marasa laifi, cewar rahoton Hindu.

A nasa bangaren, Firaministan India Narendra Modi ya taya shugaban Iran murnar bukukuwan Eid da Nowruz, tare da fatan zaman lafiya da ci gaba a yankin.

Ya nuna damuwa kan yadda rikicin ke kara tsananta, yana mai jaddada bukatar a kare zaman lafiya da kwanciyar hankali a Gabas ta Tsakiya.

Modi ya kuma yi Allah wadai da hare-haren kan muhimman kayayyakin more rayuwa, yana mai cewa hakan na barazana ga tattalin arzikin duniya.

Ya jaddada muhimmancin tsaron hanyoyin ruwa, musamman mashigan Hormuz, domin tabbatar da cewa jiragen ruwa na kasuwanci na ci gaba da zirga-zirga cikin aminci.

Shugaban Iran ya tattauna da Emmanuel Macron

A baya, an ji cewa shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi magana game da kiran a tsagaita wuta a yakin da kasar ke yi da Isra'ila.

Kara karanta wannan

China ta gaza hakuri, ta sake yunkurowa kan yakin Amurka da kasar Musulunci ta Iran

Pezeshkian ya ce tattaunawar tsagaita wuta ba ta da amfani muddin babu tabbacin cewa ba za a sake kai hare-hare ba.

Ya bayyana hakan ne bayan tattaunawa da shugaban Faransa, Emmanuel Macron, inda ya zargi Amurka da Isra'ila da kai hari kan Iran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.