An Yi Yunkurin Sasanta Amurka da Iran, Sakamakon Bai Yiwa Kasashe 2 Dadi ba
- Kasashe biyu a Gabas ta Tsakiya sun yi yunkurin kawo karshen musayar wutar da ake yi tsakanin Amurka, Isra'ila da kaasar Iran
- Sai dai yayin da kasashen suka tuntubi gwamnatin Amurka da ta Iran domin komawa teburin tattaunawa, lamarin bai masu dadi ba
- Rahotanni sun nuna cewa Amurka da Iran sun nuna ba su da sha'awar komawae teburin sulhu domin tsagaita wuta a yakin da ke gudana
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Amurka - Gwamnatin Shugaba Donald Trump ta ƙasar Amurka ta yi watsi da yunƙurin wasu ƙasashen Gabas ta Tsakiya na fara tattaunawar diflomasiyya domin kawo ƙarshen yaƙin da ake yi da Iran.
Rahotanni daga majiyoyi masu tushe sun ce ƙasashe da dama sun yi ƙoƙarin shiga tsakani domin tsagaita wuta, amma gwamnatin Trump ta nuna cewa ba zai yiwu ba a yanzu.

Kara karanta wannan
Ministan tsaro ya faɗi dalilin da ya sa ƴan ta'adda suka fi kai hare hare a Ramadan

Source: Twitter
Iran ta ƙi yarda ta zauna da Amurka
A bangaren Tehran, majiyoyi biyu daga cikin manyan jami’an Iran sun shaidawa Reuters cewa ƙasar ba za ta amince da batun tsagaita wuta ba har sai Amurka da Isra’ila sun dakatar da duk hare-haren da suke kaiwa.
Iran ta kuma gabatar da wasu sharuɗɗa kafin ta amince da sulhu, ciki har da dakatar da hare-haren Amurka da Isra’ila gaba ɗaya da biyan diyya kn asarar da yakin ya haifar.
Kasashen da suka yi yunkurin sulhunta Iran da Amurka
Ƙasashen da suka yi ƙoƙarin shiga tsakani sun haɗa da Oman, wacce ta taba shirya tattaunawar Iran da Amurka kafin yaƙin, da Masar da ita ma ta yi ƙoƙarin sake buɗe zaman tattaunawa.
Sai dai majiyoyi sun ce Fadar White House ta bayyana cewa Shugaba Trump yana so ya ci gaba da kai farmaki domin ƙara raunana ƙarfin sojojin Iran.
Wani jami’i a gwamnatin Amurka ya ce:
“Shugaban kasa ba ya sha’awar tattaunawa a yanzu. Za mu ci gaba da wannan yakin ba tare da tsayawa ba.”
Donald Trump na iya fuskantar matsin lamba
Wasu a Amurka na gargadin cewa tsawon lokacin da za a dauka a yaƙin na iya jefa gwamnatin Trump cikin matsin lambar siyasa, musamman saboda tashin farashin fetur da karatowar zaɓukan majalisar dokokin Amurka.
Sai dai wasu masu ba shi shawara suna ƙarfafa shi da ya ci gaba da yaƙin domin lalata shirin makamai masu linzami na Iran da hana ta mallakar makamin nukiliya, cewar rahoton tashar Al-Jazeera.

Source: Getty Images
Duk da yunƙurin sasanci daga wasu ƙasashe, bangarorin biyu na ƙara tsaurara matsayinsu, lamarin da ke nuna cewa yaƙin na iya ɗaukar lokaci mai tsawo kafin a samu mafita.
Jagoran addinin Iran ya shirya daukar fansa
A wani rahoton, kun ji cewa jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei ya sha alwashin daukar fansar mahaifinsa da sauran wadanda suka yi shahada a yakin Isra'ila/Amurka.
A jawabin da ya yi, Mojtaba ya yi kira ga al’ummar kasar su hada kai, tare da amincewa da wahalhalun da ake fuskanta sakamakon yakin da Iran ke yi.
Sabon jagoran ya tabbatar wa ‘yan kasar cewa Iran ba za ta manta da wadanda aka kashe ba, yana mai cewa za a dauki fansar wadanda ya kira “shahidai."
Asali: Legit.ng

