Dara Ta Ci Gida: Amurka Ta Kakkabo Jirginta Marar Matuki bisa Kuskure a Texas

Dara Ta Ci Gida: Amurka Ta Kakkabo Jirginta Marar Matuki bisa Kuskure a Texas

  • Sojojin Amurka sun kakkabo wani jirgi marar matuki na hukumar fasa-kwaurin kasar bisa kuskure ta hanyar amfani da na'urar laser
  • Hukumar FAA ta dakatar da zirga-zirgar jirage a yankin Texas sakamakon fargabar hatsarin da wannan fasahar laser ke haddasawa
  • 'Yan majalisar Amurka sun soki gwamnati kan rashin hadin kai tsakanin hukumomin tsaro da ya kai ga kuskuren kakkabo jirgin kasar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Amurka - Sojojin Amurka sun kakkabo wani jirgi marar matuƙi na hukumar fasa-kwauri da kiyaye iyakoki ta CBP ta hanyar amfani da na'urar laser.

Wannan kuskure ya tilasta wa hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama (FAA) dakatar da dukkan tashi da saukar jiragen sama a yankin Fort Hancock da ke jihar Texas a ranar Alhamis.

Amurka ta kakkabo jirginta marar matuki

Rahoton kamfanin labaran DW ya nuna cewa Pentagon ta yi amfani da wannan makamin laser ne domin kakkabo jirgin a kusa da iyakar Mexico, a wani yanki da ƙungiyoyin safarar miyagun ƙwayoyi ke yawan turo nasu jiragen.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun firgita kauyukan Bauchi, mutane sun shiga gudun hijira

Hukumomin Pentagon, FAA, da CBP sun fitar da haɗaɗɗiyar sanarwa inda suka bayyana cewa sojoji sun yi amfani da tsarin ne domin "kakkabo wani jirgi da suka ga yana shawagi a saman sansanin sojoji".

Sun ƙara da cewa lamarin ya faru ne a wani wuri wanda ya kebanta daga mutane, kuma babu jiragen da ake sufuri da su a kusa da yankin.

'Yan majalisa sun caccaki Pentagon

Sai dai, wasu manyan ƴan majalisar dokoki na jam'iyyar Democrat sun soki wannan lamari, inda suka bayyana shi a matsayin "rashin ƙwarewa" da kuma rashin haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro.

Dan majalisa Rick Larsen, Bennie Thompson da Andre Carson da ke cikin kwamitocin kula da sufurin jiragen sama da harkokin tsaron cikin gida ne suka yi wannan suka.

Sanarwar hadin gwiwa ta ƴan majalisar ta bayyana:

"Yanzu muna ganin sakamakon rashin ƙwarewa. Mun yi gargaɗi tun watanni da suka gabata kan rashin horar da masu sarrafa waɗannan na'urori, amma aka yi kunnen uwar shegu da mu."

Sabani tsakanin hukumomin Amurka

Wannan hatsari ya sa FAA faɗaɗa iyakokin da aka haramta wa jirage zuwa yanzu domin tabbatar da tsaro. a cewar rahoton Reuters.

Kara karanta wannan

Amnesty ta hurawa Abba Kabir wuta a Kano, ta zarge shi da cin zarafin 'yan adawa

A farkon wannan watan ma, an samu matsala makamanciyar wannan a filin jirgin El Paso, inda aka dakatar da zirga-zirga na tsawon sa'o'i takwas saboda fargabar amfani da wannan makamin na laser.

Sanata Tammy Duckworth ta yi kira ga masu bincike na cikin gida da ke karkashin hukumomin uku da su gudanar da bincike na musamman kan wannan kakkabo jirgi da kuma abin da ya faru a El Paso.

Majiyoyi sun bayyana cewa Pentagon da CBP sun yi imanin za su iya amfani da laser ba tare da neman izinin FAA ba, lamarin da ya haddasa rashin haɗin kai tun farko.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com