‘A Tsorace Suke’: Issa Tchiroma Ya Zargi Gwamnatin Kamaru da Sace Iyalansa
- Jagoran adawa na Kamaru, Issa Tchiroma Bakary, ya zargi gwamnati da kulla shirin tsoratar da yan adawa a kasar
- Hakan ya biyo bayan zaben shugaban ƙasa da aka gudanar a ranar 12 Oktobar 2025 wanda jagoran adawar ya ce ya lashe
- Tchiroma ya bayyana cewa an sace mutane biyu daga danginsa da kuma mai dafa masa abinci a Garoua da ke kasar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Garoua, Cameroon - Jagoran adawa na Kamaru, Issa Tchiroma Bakary, ya zargi gwamnati da kulla shirin zalunci, kisa da garkuwa da mutane.
Tchiroma ya ce hakan na faruwa ne bayan zaben shugaban ƙasa da aka gudanar a watan Oktobar 2025 da dan adawar ya yi ikirarin shi ne ya yi nasara.

Source: Getty Images
Zargin da Tchiroma ke yi wa gwamnatin Kamaru
Hakan na cikin wata sanarwa a safiyar Jumma’a 31 ga watan oktobar 2025 da jaridar Daily Trust ta samu.

Kara karanta wannan
Abin boye ya fito fili: Gwamnatin Tinubu ta faɗi dalilin sassauci ga Maryam Sanda
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tchiroma ya bayyana cewa an sace mambobi biyu na danginsa da kuma mai dafa masa abinci a garin Garoua a ranar Laraba da daddare.
Ya ce:
“Sun mayar da wannan abu tamkar yaki ne a kan al’ummar Kamaru, suna amfani da kisa, zalunci, da tsoratarwa don su ci gaba da mulki saboda tsoron abin da zai same su idan suka sauka.
“Ina bukatar a sako iyalina da aka sace da kuma duk wanda aka kama ba bisa ƙa’ida ba.”

Source: Getty Images
Alwashin da Tciroma ya ci a Kamaru
Har ila yau, a cikin wata sabuwar sanarwa da aka fitar ranar Juma’a, jagoran adawar ya tabbatar da cewa ya bar gidansa a Garoua, yanzu yana ƙarƙashin kariyar “sojojin da ke tare da shi”.
Ya sake jaddada cewa zai ci gaba da kalubalantar gwamnatin yanzu tare da yin kira ga ’yan ƙasarsa da ke tsare da su ƙara jajircewa, cewar Africanews.
“Ina kira ga wadanda aka kama da wadanda aka sace: ku kasance masu ƙarfin zuciya, ba zan gajiya ba sai wannan gwamnati ta dawo muku da nasara.
“Ina godiya ga sojojin kishin ƙasa da suka nuna halin jarumta wajen kai ni wurin da ya fi aminci, kuma yanzu suna kula da tsarona, zan yi jawabi na musamman cikin ’yan mintuna.”
- Issa Tchiroma Bakary
Ana dai samun tashin hankali a yankin Arewacin Kamaru bayan wannan lamari, inda jami’an tsaro suka ƙara tsaurara matakai, yayin da kungiyoyin kare hakkin dan Adam ke bayyana damuwa kan kama mutane ba tare da dalili ba.
Gwamnatin Kamaru za ta hukunta Tchiroma
Kun ji cewa Gwamnatin Kamaru ta ce za ta dauki matakin shari’a kan jagoran adawa, Issa Tchiroma Bakary bisa zargin tayar da tarzomar bayan zaben shugaban kasa da aka yi.
Akalla mutane hudu aka kashe yayin arangama tsakanin jami’an tsaro da magoya bayan 'yan adawa tun bayan zaben shugaban kasa a ranar 12 ga watan Oktobar 2025.
Ministan cikin gida Paul Atanga Nji ya ce wasu daga cikin masu taimaka wa Bakary wajen shirya tarzomar ma za su fuskanci hukunci.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
