Maria Machado: Mace Ta Buga Trump da Kasa wajen Samun Kyautar Nobel a 2025

Maria Machado: Mace Ta Buga Trump da Kasa wajen Samun Kyautar Nobel a 2025

  • Kwamitin Nobel Prize ya bai wa ‘yar fafutukar dimokuradiyyar Venezuela, Maria Corina Machado, kambun zaman lafiya na 2025
  • Machado ta samu girmamawar ne saboda jajircewarta wajen kare ‘yancin jama’ar, Venezuela da neman sauyi daga mulkin danniya
  • Shugaban Amurka, Donald Trump na cikin mutanen duniya da suka sanya rai wajen samun girmamawar a bana amma ba su samu ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Norway – Kwamitin Nobel Prize ya sanar da cewa ‘yar siyasa mai fafutukar kare dimokuradiyya daga ƙasar Venezuela, Maria Corina Machado, ce ta lashe kambun zaman lafiya na 2025.

Machado ta samu lambar yabon ne saboda ƙoƙarinta wajen kare ‘yancin ɗan adam da neman sauyi cikin lumana daga mulkin kama-karya zuwa tsarin dimokuradiyya a ƙasarta.

Maria Corina Machado da Trump
Maria Corina Machado da ta doke Trump wajen samun kambun zaman lafiya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Kwamitin ya bayyana a X cewa Maria mace ce mai ƙwazo da jarumtaka wadda ke ci gaba karfafa dimokuradiyya.

Kara karanta wannan

Ana batun kisan kiyashin Kiristoci, CAN ta aika sako ga gwamnatin tarayya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin ba Maria kambun zaman lafiya

Kwamitin Nobel ya ce Maria Machado ta kasance jagorar kare dimokuradiyya a Venezuela, kuma ta zama abin koyi wajen nuna ƙarfin hali a fagen siyasar yankinta.

Tun sama da shekaru 20 da suka gabata ta kafa ƙungiyar Súmate, wacce ke fafutukar tabbatar da sahihan zaɓe.

Duk da barazanar kama ta, tsarewa da tsangwama daga gwamnati, Machado ta ci gaba da kare ‘yancin jama’a da neman gaskiya ga al’ummarta.

Yanayin siyasa a kasar Venezuela

Venezuela, wacce a baya ta kasance ƙasa mai wadata da ke bin tsarin dimokuradiyya ta koma ƙasar da ke fama da talauci da zalunci.

Wani rahoto ya nuna cewa fiye da mutane miliyan 8 ne suka bar ƙasar saboda matsin tattalin arziki da siyasa.

An ce gwamnatin kama-karya ta ci gaba da amfani da ƙarfi wajen murkushe ‘yan adawa, da yin maguɗin zaɓe, da tsare masu fafutuka.

Hoton Maria Corina Machado
Maria Corina Machado da ta lashe kambun zaman lafiya na 2025. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A zaɓen 2024, an hana Maria Machado tsayawa takarar shugaban ƙasa, sai ta goyi bayan Edmundo Gonzalez Urrutia, wanda ya samu goyon bayan jama’a a faɗin ƙasar.

Kara karanta wannan

Abin da Mahmood Yakubu ya fadawa Tinubu a takardar ajiye shugabancin INEC

‘Yan adawa sun yi aiki cikin haɗin kai, suka tattara sakamakon zaɓe, suka kuma tabbatar da cewa jama’a sun zabi ra’ayinsu.

Shugaba Trump ya so samun kyautar Nobel

A gefe guda, Aljazeera ta rahoto cewa shugaban Amurka Donald Trump ya nuna sha'awar samun kambun a lokuta daban daban.

Trump, wanda ya dade yana nuna sha’awar samun kambun zaman lafiya, ya ce ya kamata a yaba masa saboda ya tsayar da yaƙe-yaƙe takwas cikin wata tara.

An rahoto Trump ya ce:

"Na ceci rayuka da dama, ba don samun kambun na yi ba,"

Ministan harkokin kasuwanci na Amurka, Howard Lutnick, ya bayyana cewa:

“Ba shakka Trump ya cancanci kambun saboda shirin zaman lafiya na Gaza.”

Haka kuma, ɗansa Eric Trump ya roƙi jama’a su yada rubutunsa a X idan suna ganin mahaifinsa ya cancanci wannan girmamawa.

Trump ya ce an tsayar da yakin Gaza

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya sanar da cewa an amince da shirin tsagaita wuta a Gaza.

Kara karanta wannan

Rigiji gabji: Atiku ya nemi a binciki Tinubu da ministocinsa kan takardun bogi

Hakan na zuwa ne bayan fara tattaunawa da aka yi a kasar Masar tsakanin kungiyar Hamas da Isra'ila.

Shugaba Trump ya bayyana cewa sannu a hankali za a bayyana sauran matakan da za a dauka domin kawo cikakkiyar zaman lafiya a Gaza.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng