Nukiliya: Iran Ta Bayar da Sharadin Komawa Teburin Tattaunawa da Amurka
- Iran ta gargadi Amurka da kada ta sake kai wani hari idan tana son komawar tattaunawa kan shirinta na mallakar makamin nukiliya
- Wannan na zuwa bayan an kawo karshen yakin kwanaki 12 da aka gwabza tsakanin Isra'ila da Iran da Amurka da shiga daga bayana
- Amurka ta shiga rikicin kai tsaye a ranar 21 ga Yuni, inda ta kai farmaki wuraren nukiliya uku a Iran da suka hada da Fordo, Natanz da Isfahan
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kasar Iran – Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Iran, Majid Takht-Ravanchi, ya bayyana cewa dole ne Amurka ta fitar da yiwuwar kai karin hare-hare a Iran.
Wannan na daga cikin sharadin da ta bayar matukar ana son a ci gaba da zama domin tattauna batun mallakar makamin nukiliya da ta ke yi.

Asali: Getty Images
BBC ta ruwaito Majid Takht-Ravanchi ya ce gwamnatin Donald Trump ta isar da saƙo ga Iran ta hannun masu shiga tsakanin cewa tana son dawo da teburin sulhu a wannan makon.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amurka da Iran sun fara tattaunawa kan shirin nukiliyan Iran ne kafin Isra’ila ta kai hari kan wuraren nukiliya da cibiyoyin soja na Iran a farkon wannan watan.
Amurka ta kai hari a kasar Iran
The Indian Express ta bayyana cewa Amurka ta shiga wannan rikici kai tsaye a ranar 21 ga Yuni, inda ta yi wa wuraren nukiliya guda uku na Iran ruwan bama-bamai.
Takht-Ravanchi ya ce Iran ba za ta daina kokarin haɓaka sinadarin uranium don dalilai ci gaban kanta ba, yana mai karyata zargin cewa tana kokarin ƙera makamin nukiliya a boye.
Ya ce Iran ta shafe lokaci tana fuskantar ƙalubalen samun sinadarai don gudanar da bincike, wanda ya sa dole ta dogara da kanta wajen ci gaba da cika burinta.
Yadda Isra’ila ta kai hari a Iran
Isra’ila ta kai farmaki a ranar 13 ga Yuni, inda ta kai hare-hare kan wuraren nukiliya da na soja, tare da kisan gilla ga jami’an soja da masana kimiyya a Iran.
A ranar Litinin, Iran ta bayyana cewa bisa ga bayanan binciken kwararru na baya-bayan nan, mutane 935 ne suka mutu sakamakon hare-haren Isra’ila.
A gefe guda kuma, ma’aikatar lafiyar Isra’ila ta tabbatar da mutuwar mutane 28 a ƙasar tun daga 13 ga Yuni, lokacin da Iran ta mayar da martani da kai hari a Isra’ila.

Asali: Getty Images
Ranar 21 ga Yuni, Amurka ta shiga cikin rikicin, inda ta kai farmaki a wuraren nukiliya uku da suka hada da Fordo, Natanz da Isfahan.
Takht-Ravanchi ya ce ba zai iya bayyana cikakken hasarar da Iran ta yi ba, amma hare-haren sun shafi ayyukan su na ci gaban nukiliya.
Iran ta kashe yan leken asirin Isra'ila
A baya, mun ruwaito cewa Hukumomin Iran sun tabbatar da cewa sun kama daruruwan mutane da ake zargi da leken asiri, tare da zartar da hukuncin kisa ga wasu daga cikinsu.
Iran na zargin bayanan sirri da aka bai wa Isra’ila na da nasaba da kashe-kashen wasu manyan jami’an rundunar sojin kasar da aka kai musu farmaki yayin rikicin baya-bayan nan.
Wasu daga cikin wadanda aka kashe sun hada da manyan hafsoshi daga rundunar IRGC da kuma masana kimiyyar nukiliya, a cikin kwanaki 12 da aka shafe ana musayar bama-bamai.
Asali: Legit.ng