An Kwantar da Sarki Charles a Asibiti, Cikakken Bayanai Sun Fito

An Kwantar da Sarki Charles a Asibiti, Cikakken Bayanai Sun Fito

Landan - An kwantar da Sarkin Burtaniya, Charles III a wani asibitin kudi na Landan a ranar Juma'a don yi masa tiyata a mafitsara, kamar yadda fadar Buckingham ta sanar.

Fadar ta ruwaito cewa rashin lafiyar sarkin tsananta, amma a ranar Juma'a ta ce basaraken na samun sauki yayin da ake shirin yi masa tiyata.

Rashin lafiyar Sarkin Burtaniya, Charles, ta tsananta, an kwantar da shi a asibiti.
Rashin lafiyar Sarkin Burtaniya, Charles, ta tsananta, an kwantar da shi a asibiti. Hoto: Pool
Asali: Getty Images

A cewar masarautar:

"Mai martaba na yi wa daukacin wadanda suka aika masa da sakon neman lafiya godiya."

Masarautar dai ba ta bayar da wani karin bayani dangane da halin da sarkin ya ke ciki ba, kuma ba a san tsawon wanne lokaci zai dauka a asibitin yana jinya ba, a cewar CBS News.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Reuters ta ruwaito cewa an ga sarkin ya shiga asibitin da ke yammacin Landan tare da sarauniyarsa Camilla, inda Kate, sarauniyar Wales ita ma ke jinya bayan yi mata tiyata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel