Isra’ila da Falasdinu: Kungiyar Shi’a Ta Tura Gargadi Ga Tinubu Kan Ta’addancin Isra’ila

Isra’ila da Falasdinu: Kungiyar Shi’a Ta Tura Gargadi Ga Tinubu Kan Ta’addancin Isra’ila

  • Kungiyar Shi’a a Najeriya ta kirayi gwamnatin Najeriya da ta yanke duk wata alaka da ta ke kullawa ko ta kulla da kasar Isra’ila ta ko wane bangare
  • Kungiyar ta bayyana haka a Abuja inda ta koka kan yadda haramtacciyar kasar Isra’ila ke musgunawa Falasdinawa tsawon shekaru 75
  • Farfesa Abdullahi Danladi, shugaban kwamiti kwararru a kungiyar ya yi Allah wadai da wannan cin zarafi da ake ci gaba da yi wa Falasdinu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Kungiyar ‘yan Shi’a a Najeriya ta gargadi Gwamnatin Tarayya kan ci gaba da alaka da Isra’ila.

Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da gwabza yaki tsakanin Isra’ila da kungiyar Hamas.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Jigon Jam’iyyar PDP a Najeriya Ta Riga Mu Gidan Gaskiya, Jam’iyyar Ta Shiga Dimuwa

Shi'a ta gargadi Tinubu kan ci gaba da alaka da Isra'ila
Kungiya Shi'a ta tura sako ga Tinubu kan Isra'ila. Hoto: Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Twitter

Meye kungiyar Shi’a ke cewa kan Isra’ila, Tinubu?

A yayin wata ganawa da manema labarai, shugaban kwamitin kwararru a kungiyar, Farfesa Abdullahi Danladi ya yi Allah wadai da yadda Isra’ila ke kai farmaki Gaza ba kakkautawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Danladi ya ce sun taru a wannan wuri ne don tabbatar wa ‘yan Najeriya irin cin zarafin da Isra’ila ke yi kan Falasdinawa, Daily Trust ta tattaro.

Ya ce:

“Makasudin taruwarmu a nan shi ne mu tabbatar wa mutanen Najeriya da sauran jama’a irin ta’addanci da haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi kan Falasdinu.
“Ya tabbata shugabanmu, Sheikh Ibrahim Zakzaky na jagorantar yaki da cin zarafin Falasdinu da sauran marasa karfi a duniya.”

Wane gargadi Shi’a ta yi wa Tinubu kan Isra’ila?

Ya kara da cewa wanna abin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya na mamayar Falasdinu ya kara bude wani shafi na tarihi a duniya, Platinum Post ta tattaro.

Kara karanta wannan

Da Dumi: Bayan Shan Kaye a Kotun Koli, Shugaban LP na Kasa Ya Sallami Hadimansa 5

Farfesan ya ce tsawon shekaru 75 Isra’ila na cin zarafi tare da tilasta Falasdinawa barin gidajensu karkashin kulawar munafukar kasa Amurka.

Ya kirayi Gwamnatin Najeriya da ta yanke duk wata alaka da ta ke kullawa ko ta kulla da kasar Isra’ila ta ko wane bangare.

Kungiyar Shi’a ta yi zanga-zangar goyon bayan Falasdinu

A wani labarin, Kungiyar Shi’a a Najeriya ta yi zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinu a babban birnin Tarayya, Abuja.

Kungiyar ta yi zanga-zangar ce yayin da ake ci gaba da gwabza fada tsakanin Isra’ila da kungiyar Hamas a yankin Gabas ta Tsakiya.

Ta yi Allah wadai da hare-haren ta’addanci da Isra’ila ke kai wa kan Gaza cikin ‘yan kwanakin nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel