'Yan Shi'a Sun Yi Allah-Wadai Da Harin Bam a Cocin Gaza

'Yan Shi'a Sun Yi Allah-Wadai Da Harin Bam a Cocin Gaza

FCT, Abuja - Kungiyar 'Islamic Movement of Nigeria (IMN)' a ranar Juma'a ta yi zanga-zanga kan harin da aka kai cocin 'Greek Orthodox Saint Porphyrius Church' da ke Gaza yayin da rikici ke cigaba da wanzuwa tsakanin Isra'ila da Falasdinu.

Al Jazeera ta ambato ministan harkokin cikin gida na Falasdinu yana cewa harin sama da Isra'ila ta kai ya raunta 'mutane da dama' tare da jikkata wadanda suka fake a harabar cocin a Gaza.

Ofishin watsa labarai na gwamnatin Hamas da ke mulkar Gaza, a ranar Juma'a ta rahoto cewa Kiristoci Falasdinawa 18 suna cikin wadanda suka rasu.

Daily Trust ta rahoto cewa IMN ta yi zanga-zangan ne a Babban Masallacin Kasa a Abuja bayan salla.

A cikin sanarwa da ya fitar, Sheikh Sidi Munir Mainasara, mamba na kungiyar, ya yi kira ga yan Najeriya su goyi bayan mutanen Falasdinu da ake 'musgunawa'.

Kara karanta wannan

Mista Ibu: Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki Ya Dauki Nauyin Asibitin Jarumin Da Ke Jinya

"Mun yi zanga-zanga yau don tir da harin sama da Isra'ila ta kai cocin Greek Orthodox Saint Porphyrius Church da ke birnin Gaza, Palestine. Da ke birnin Gaza mai dimbin tarihi wanda shine coci mafi tsufa a garin. Tsawon shekaru cocin ya kasance mafaka ga mutane masu mabanbantan addini. Abin ya faru daren jiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Hakan na zuwa ne bayan harin asibitin Gaza wanda ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 500. Mun yi imanin wannan kisar gilla ne kuma ya saba dokokin kasa da kasa.
"Muna kira ga yan Najeriya su goyi bayan yan Falasdinu. Goyon bayan wadanda ake zalunta mutuntaka ne. Kamar yadda Marin Luther King Jr ya ce, zalunci a ko'ina barazana ce ga adalci a ko'ina. Muna cikin alaka da ba za mu iya tserewa ba. Duk abin da ya shafi daya, ya shafi saura baki daya."

Kara karanta wannan

"Ku Yi Hannun Riga Da Isra'ila": Kungiyar Musulmi Ta Aika Sako Ga Kasashen Duniya Kan Yakin Gaza

Goyon bayan adalci koyarwar shugaban mu El-Zakzaky ne

Sanarwar ta cigaba da cewa:

"Kira ga al'umma su goyi bayan adalci tare da adawa da masu zalunci a ko ina na cikin koyarwar shugaban mu, Shaikh Ibrahim El-Zakzaky. Fiye da shekaru 30, IMN, karkashin jagorancin mai alfarama Shaikh Ibrahim El-Zakzaky ta kasance tana shirya zanga-zanga don goyon bayan wadanda ake zalunta a Falasdinu.
"Bisa abin da ke faruwa, muna kira ga dukkan yan Najeriya su bude baki su nuna goyon bayansu ga Falasdinawa da ake zalunta.
"Mun yi tir da harin asibitin Gaza, kuma dole dora alhakin harin kan haramtaciyar kasar Isra'ila."

Asali: Legit.ng

Online view pixel