Kawai na Tashi da Niyyar Kisan Kai: Matashi ya Burmawa Direban Motar Haya Wuka
- Brandon Jacobs matashi mai shekaru 26 da ya sokawa wata direban motar da ya dauka wuka bayan ta kai shi otal
- Bayan ‘yan sanda sun kama shi tare da titsiye shi, ya sanar da cewa kawai ya tashi ranar da bukatar kashe rai, abun kuma ya kare kanta
- An gano cewa, wacce ya kashen mai suna Sheriff Joseph Lopinto ma’aikaciya ce da sashen kasafi na ‘yan sandan New Orleans
Wani matashi mai suna Brandon Jacobs ya halaka wata dattijuwar direban mota mai suna Yolanda Dillion, jaridar Vanguard ta rahoto.
Kafin halaka Yolanda, ma’aikaciya ce New Orleans ’yan sanda wacce ke aikin tuki bayan tashi daga aiki.
Kamar yadda rahoto ya bayyana, Brandon ya sokawa Yolanda wuka har ta mutu daga bayan motar ta dake Louisiana a Amurka bayan ta dauke shi a ranar Alhamis.
A yayin da yake tafe zuwa dakin otal din da ya kama kafin ta kai shi, ‘yan sanda sun kama shi kan zargin aikata laifin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Makashin ya wallafa bidiyon kisan a Facebook inda da aka tambaye shi yace:
“Kawai ya so kashe wani ne.”
A wani taron manema labarai, Sheriff Joseph Lopinto ya tabbbatar da cewa an halaka Yolanda kuma ya bayyana cewa lamarin lamarin ya faru ne a ranar Alhamis.
Lopinto yayi bayanin cewa:
“A bayanin wanda ake zargin, yace ya tashi a safiyar jiya kuma ya yankewa kan shi hukuncin cewa zai kashe wani kuma yace abinda zai yi kenan ranar.
“Mun tambaye shi takamaiman yadda ya dauketa, yace bai dauke ta ba ita ce direba kuma ta dauke shi.
“Yana zaune a kujerar baya ya soka mata wuka. Ya fice daga motar tare da yin gaba.”
Wacece Yolanda?
Yolanda wacce ke aiki a bangaren kasafi na ‘yan sandan ta kasance abar soyuwa a zukatan abokan aikinta.
SP Shaun Ferguson yace:
“Za a yi matukar kewarta. Ta kasance mai shiru-shiru da kirki. Ta kasance ta musamman a wannan sashen kuma mutuwarta ta taba zukatan ma’aikata.”
Wata takardar da Jefferson Parish ta kara da cewa an kama wanda ake zargin cikin sa’o’i kadan da yayi kisan kan.”
Sun ce:
“Bincikenmu ya nuna cewa wacce aka kashe din direba ce da ta dauko Jacob daga wani wuri a New Orleans zuwa wani otal.
“Yayin da ta kai shi, Jacobs ya doka mata wuka ba sau daya ba kafin ya bar ta a motar.”
’Dan Chana ya sokawa budurwarsa wuka
A wani labari na daban, wani ‘dan Chana mazaunin garin Kano ya sokawa Budurwarsa mai suna Ummu Kulsum Buhari wuka a Jambulo.
An gano cewa har gida ya risketa tare da burma mata wuka inda ta mutu kafin a kai ta asibit.
Asali: Legit.ng