Wata Mata 'Yar Asalin Najeriya Ta Zama Janar A Rundunar Sojin Amurka
- Amanda Azubuike, wata yar asalin Najeriya ta samu karin girma zuwa mukamin Birgediya Janar a Rundunar sojin Amurka
- An haifi Azubuike ne a Landan a shekarar 1994, bayan iyayenta sun bar Najeriya sun koma Birtaniya kuma ta fara aiki a matsayin matukiyar jirgi a sojin Amurka
- Bayan shekara 11 a matsayin matukiyar jirgin sama, ta rike manyan mukamai da dama a rundunar sojin Amurka musamman a bangaren sadarwa
Amurka - Wata mata wacce asalinta yar Najeriya ce, Amanda Azubuike, ta samu karin girma zuwa Birgediya Janar a rundunar sojojin Amurka a Fort Knox, Kentucky, Amurka, The Punch ta rahoto.
An haife ta Landan, Birtaniya, ga iyaye 'yan Najeriya, Azubuike ta shiga rundunar sojin Amurka a shekarar 1994 kuma ta zama matukiyar jirgi bayan ta ci Darasin Farko na Jami'an Jirgin Sama.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Da ya ke tsokaci kan iya shugabancinta, Kwamanda a Rundunar Sojin Amurka, Janar James Rainey ya ce Azubuike 'na kawo cigaba ga duk wanda ke zagaye da ita.'
Bayan aikinta na shekaru 11 a matsayin matukiyar jirgin sama, ta cigaba da aiki a rundunar sojoji a matsayin jami'ar hulda da jama'a.
Mukaman da Janar Azubuike ta rike
A halin yanzu Azubuike na aiki a matsayin mataimakiyar kwamanda a Rundunar sojin Amurka kuma a baya ta yi aiki a matsayin babban mashawarciya a ofishin sakataren tsaro.
Ta kuma yi aiki matsayin babban jami'ar hulda da jama'a a United States Southern Command, Fort Lauderdale kuma direktan sashin hulda da jama'a, a hedkwatar dakarun hadin gwiwa a Washington.
Ta kuma yi aiki a matsayin Mashawarciyar Sadarwa ga Kungiyar 'Yan Wasan Kwallon Kafa ta Kasa da ma'aikaciyar Hulda da Jama'a na NFL, Washington Redskins.
Takaitaccen tarihin karatun Janar Azubuike
Baya ga aikin soja, Janar Azubuike tana da digirin farko a kimiyyar sadarwa/nazarin kafafen watsa labarai daga Jami'ar Central Arkansas, da digiri na biyu a Tsaron Kasa da Dabaru daga Jami'ar Yaki ta Amurka, da kuma wani digirin na biyu a Hulda da Jama'a/Kamfanoni daga Jami'ar Georgetown.
'Yar baiwa: Wata yarinya 'yar asalin Najeriya ta kammala karatun PhD tana da shekaru 14
A 2015, labarin wata yar shekara 10 da ta kware a fannin lissafi, Esther Okade wacce iyayenta suka kasance yan Najeriya, ya bazu a kafofin yada labaran kasashen ketare.
A cewar rahotonni, Esther wacce ke da zama a Walsall, wani gari mai masana’antu a kasar Birtaniya, bata halarci makaranta ba a waje, illa kawai mahaifiyarta da ke koyar da ita a gida. Mahaifiyarta Omonefe Okade wacce ake kira Efe, ta kasance malamar makaranta kuma kwararriya a fannin lissafi.
Asali: Legit.ng