Mai dokar barci ya buge da gyangyadi: Mai hukunta mazinata ya sha bulala saboda ya yi zina
Mai dokar barci ya buge da gyangyadi, ana zaton wuta a makera, sai ga shi an tsinceta a masa, wani mutumi dan asalin kasar Indonesiya dake aiki a majalisar malamai ta garin Aceh ya shiga hannu bayan an kamashi da laifin zina.
Shi dai wannan mutumi mai suna Mukhlis bin Muhammad mai shekaru 28 ya kasance guda daga cikin jami’an majalisar malamai na yankin Aceh a kasar Indonesiya dake dabbaka tsarin shari’ar Musulunci, inji rahoton BBC Hausa.
KU KARANTA: Da dumi dumi: Kotun daukaka kara ta fatattaki dan majalisar APC daga jahar Bauchi
Majiyar Legit.ng ta ruwaito daga cikin aikin majalisar shi ne tsara daftarin dokokin hukunta laifukan zinace zinace da luwadi masu tsaurin gaske, inda ake hukunta duk wanda aka kama da wannan laifi da hukuncin bulala a bainar jama’a.
Sai dai a nan an kama mai kamawa, bayan an kama Mukhlis tare da wata mata suna saduwa da juna a cikin wata mota a daidai wani wurin shakatawa a watan Satumbar da ta gabata, wanda hakan yasa aka gurfanar dashi gaban majalisar.
Daga karshe majalisar ta yanke masa hukuncin bulala, inda a ranar Alhamis, 31 ga watan Oktoba aka zartar masa da hukuncin bulala 28, yayin da aka matar bulala 23 a bainar jama’a, sa’annan majalisar ta yanke hukuncin sallamarsa daga aiki.
Mataimakin magajin garin Aceh, Hussaini Wahab ya bayyana cewa: “Wadannan dokokin Allahne, duk wanda aka kama da laifi dole a hukunta shi ko da dan kungiyar MPU ne.” Inji shi.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng