Wasu Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Wani Masallaci A Jihar Enugu

Wasu Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Wani Masallaci A Jihar Enugu

  • Harin Wanda aka kai yau yayin da msallatan ke gudanar da ibada, wacce akeyi da asubh
  • An kama wasu ‘yan bindiga biyu da ke zargi da hannu wajen kashe tsohon kwamishina, a jihar Enugu
  • A 'yan kwannan, ana yawan samun kai hare-hare a dai-daiku ko a cikin jama'a a jihar Enugu

Enugu: Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba da safiyar Juma’a, sun kai hari a wani masallaci da ke Ughelli a jihar Delta, inda wasu masallata 11 suka jikkata. Kamar Yadda

Wani mazaunin garin da ya zanta da NAN ta wayar tarho, ya ce harin ya faru ne da misalin karfe 6:47 na safe a lokacin da wasu mabiya addinin Musulunci ke gudanar da sallar asuba a babban masallacin Juma’a da ke kan titin Okoroda a Ughelli.

Kara karanta wannan

Ana Shirin Zaben 2023, Tsageru Sun Cinna Wa Ofishin INEC Wuta A Fitacciyar Jihar Kudancin Najeriya

Yan Bindiga
Wasu Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Wani Masallaci A Jihar Enugu Hoto: Channels TV
Asali: UGC

Mazaunin wanda ya bayyana sunansa da Larry, ya ce da yawa daga cikin suke wwajen sun tarwatse sakamakon harbin bindiga da suka ji, da kuma ihun jama'a daga cikin masallacin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Sunana Larry, ni direba ne a nan Ughelli. Ina zaune kusa da babban masallacin Ughelli, da safiyar yau da misalin karfe 6:45 na safe muka ji karar harbe-harbe a cikin masallacin.
“Saboda tsoro, mutane da yawa kusa da gidana sun firgita kuma wasu suka shigo ciki inda daga baya kuma muka leƙo ta tagogin mu.
"Yayin da harin ya lafa, mun ji wasu na kuka mai karfi daga wasu masu ibada a cikin masallacin,"

.....in ji Larry.

A cewarsa, bayan da maharan suka fita, da yawan mazauna garin sun yi dafifi zuwa masallacin domin ganin abin da ya faru.

Kara karanta wannan

Talaka ya yi nasara: Abin da 'yan Najeriya ke cewa bayan da Aisha Buhari ta janye kara kan Aminu

Ya ce mazauna yankin sun taimaka wajen kwashe wadanda suka jikkata, ya kuma ce wasu daga cikin masallatan sun samu munanan raunuka.

Larry ya ce wasu daga cikin masu ibadar sun shaida wa mazauna garin cewa ‘yan bindigar sun tafi da wasu ‘yan uwansu guda uku.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Delta, DSP Bright Edafe, ya tabbatar da faruwar harin.

Ya tabbatar da cewa masallata 11 ne kawai suka jikkata a harin. Sai dai bai tabbatar da sace wasu masu ibada uku ba.

“Na kira DPO a Ughelli, ya tabbatar min da cewa mutane 11 sun jikkata a harin da aka kai a masallacin.
“Duk da haka, ‘yan sanda sun fara gudanar da bincike kan lamarin, kuma za mu sanar da ku yayin da muke kokarin gano masu laifin.

Edafe ya ce

"A yanzu ba a kama su ba amma ina mai tabbatar muku da cewa za mu abin da ya kamat."

Asali: Legit.ng

Online view pixel