Amarya Ta Fada Tashin Hankali Yayin da Aka Bindige Angonta Ranar Aurensu

Amarya Ta Fada Tashin Hankali Yayin da Aka Bindige Angonta Ranar Aurensu

  • Wata amarya ta fada mummunan tashin hankali yayin da aka bindige angonta Marco Antonio, har lahira yayin da ake tsaka da shagalin aurensu
  • An gano cewa, bisa kuskure wasu masu safarar miyagun kwayoyi suka harbe angonta a farmakin da suka so kaiwa wani abokin harkallarsu
  • Jami’an ‘yan sandan yankin sun tabbatar da cewa an harbe wani ango a wani birni na kusa da nan sai dai ana cigaba da bincike kan lamarin

Mexico - An harbe wani ango har lahira a yayin da ake tsaka da shagalin bikinsa a cikin kuskure inda aka bar wa amarya gawarsa kwance cikin jini.

Marco Antonio
Amarya Ta Fada Tashin Hankali Yayin da Aka Bindige Angonta Ranar Aurensu. Hoto daga lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Marco Antonio mai shekaru 32 yana rike da hannun matarsa yayin da yake tattaki zuwa mota bayan an daura aurensu a coci yayin da aka bindige shi a Caborca ake Mexico.

Kara karanta wannan

‘Yan Mata Sun Koka, Ana Yi Masu Aure da Tsofaffi Domin Iyayensu Su Biya Bashi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An sakankance cewa an harbi injiniyan ne a bisa kuskure kuma an yi nufin harbin wasu gungun jama’a ne dake safarar kwayoyi a birnin.

An ga hoton matarsa cike da tashin hankali a cikin jini bayan wanke mata riga da yayin yayin da take taimakon masoyinta.

‘Yar uwar Antonio ma an harbeta a bayan kamar yadda jaridun yankin suka tabbatar.

Jami’ai sun tabbatar da cewa Antonio ya sheka lahira bayan farmakin da aka kai masa da bindiga wanda ake gani a matsayin kuskure.

Carboca madaddala ce ta fitacciyar kungiyar masu safarar kwayoyi ta Caborca wacce fitaccen mai safarar kwayoyi Rafael Caro Quintero ke shugabanta. Kungiyar a halin yanzu tana dauki ba dadi da Los Salazar kan safarar kwayoyi.

Jami’i mai binciken lamarin yace:

“Bincike ya nuna cewa harin da ya samu Marco Antonio an yi nufin samu wani ne wanda ke aure a wannan ranar amma a birni mai kusanci da nan.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya Sun Cafke Manyan Kwamandojin Boko Haram a Abuja da Kano

“Babu wani sashi na bincike da aka kebance kuma duk wasu rahoton kwararru ana cigaba da karba domin samun gamsassun bayanai tare da aiwatar da abinda ya dace kan wadanda suka yi laifin.”

Hakazalika, kamar yadda LIB suka rahoto, an harbe wani ango a birni mafi kusa duk a wannan daren.

Gwamnan jihar, Alfonso Durazo yace:

“Wannan farmakin an aiwatar da shi ne saboda mutum daya kuma hakan na nufin ba da kowa zai faru ba.”

Bayan kashe 7m a shirin biki, ango ya fasa a ranar aure, ya bayyana dalilinsa

A wani labari na daban, wata mata mai suna Sasha Aristide 'yar shekara 29 da haihuwa da saurayinta, Kelvin Heyppolite sun yi shekaru 3 suna tsara yadda shagalin gagarumin bikinsu zai kasance, ashe zata fuskanci wulakanci mafi muni.

A watan Disamban 2017 ne aka sa ranar auren masoyan, sai suka fara shirye-shiryen yadda kayataccen bikin nasu zai kasance, wanda suka kiyasta za su kashe kimanin Naira 7,426,316.12.

A yadda aka sa ranar auren, zai kasance watan Yulin shekarar 2020. Duk da tsayin ranar auren da aka saka, sun cigaba da tuntubar juna har da cigaba da shirye-shiryen babbar ranar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel