Bayan kashe 7m a shirin biki, ango ya fasa a ranar aure, ya bayyana dalilinsa

Bayan kashe 7m a shirin biki, ango ya fasa a ranar aure, ya bayyana dalilinsa

- Wata mata Sasha, mai shekaru 29 da haihuwa tayi shirin babbar ranar aurenta da saurayinta, ashe tashin hankali na tafe

- Sasha da saurayinta sun yi shekaru 10 suna soyayya, tukunna aka sa ranar aurensu cikin shekaru 3 don fara shirin gagarumar ranar

- A yadda suka kiyasta, za su kashe kimanin N7,426,316.12, sai da ranar tazo, angon yaki bayyana don a daura musu auren, lamarin da ya gigita Sasha

Wata mata mai suna Sasha Aristide 'yar shekara 29 da haihuwa da saurayinta, Kelvin Heyppolite sun yi shekaru 3 suna tsara yadda shagalin gagarumin bikinsu zai kasance, ashe zata fuskanci wulakanci mafi muni.

A watan Disamban 2017 ne aka sa ranar auren masoyan, sai suka fara shirye-shiryen yadda kayataccen bikin nasu zai kasance, wanda suka kiyasta za su kashe kimanin Naira 7,426,316.12.

A yadda aka sa ranar auren, zai kasance watan Yulin shekarar 2020. Duk da tsayin ranar auren da aka saka, sun cigaba da tuntubar juna har da cigaba da shirye-shiryen babbar ranar.

Kwanci-tashi, ranar auren tazo, sai dai kash! Ango yaki bayyana, inda ya bar Sasha cikin matsanancin tashin hankali.

Kyakkyawar amaryar da tayi shigar alfarma ta sha kuka, bayan ta gama soyayya da saurayinta na tsawon shekaru 10, amma yaki bayyana a ranar aurensu.

Sasha tayi ta shirin gagarumar ranar na tsawon shekaru 3, ashe za ta fuskanci al'amarin da zai tarwatsa farincikinta.

Sasha ma'aikaciyar jinya ta hadu da Kevin Hyppolite dake aikin ofis tun shekaru 10 da suka wuce.

Take suka fada matsananciyar soyayya wadda duk masu son su suka fara musu sambarka.

Bayan saka ranar auren su ne masoyan suka fara shirin babbar ranar, don tabbatar da ba'a samu tangarda ba.

A hankali watan Yuli 2020 ya karato, inda masoyan suka cigaba da shirye-shirye da kuma tattaunawa akan yadda shagalin auren da zai ci kimanin N7,426,316.12 ba tare da haufin komai ba.

A ranar auren, Sasha da kawayenta sun yi shigar alfarma, ganin komai na tafiya yadda suka tsara.

Ta cigaba da jiran masoyin nata don a kulla auren soyayyar tasu. Bayan ta ji shiru ne ta tuntubi Kelvin wanda yayi ta ce mata yana nan tafe ashe duk ba gaskiya bane.

A haka har yamma tayi, nan ne tagane cewa ba zuwa zai yi ba. Ta shiga cikin damuwa mafi muni, kuma tayi dana sanin amincewa da shi. Bayan an tuntubi Kelvin, cewa yayi ba da gangan bane, kaddara ce tazo a haka.

KU KARANTA: An kama dan sandan da je rubuta wa wani jarababawar UTME ta 2020

Bayan kashe 7m a shirin biki, ango ya fasa a ranar aure, ya bayyana dalilinsa
Bayan kashe 7m a shirin biki, ango ya fasa a ranar aure, ya bayyana dalilinsa. Hoto daga New York
Asali: UGC

KU KARANTA: Ina alfahari da ayyukan cigaban da muka yi wa Najeriya tare da Obasanjo - Atiku

A wani labari na daban, hakika duk uwa tagari tana wahala wurin taso da ya'yanta tun yarinta har girmansu.

Sai dai ace Allah ne zaiyi sakayya kawai. Bidiyon wata mata mai sana'ar fenti, mai suna Sognan Silla ya karade kafafen sada zumuntar zamani, inda aka ga matar tana sana'arta goye da jaririnta.

A bidiyon, matar na tsaye akan wani benci tana shafawa silin din wani daki fenti. Hakika bidiyon ya karade kafar sada zumuntar zamani ta Facebook, wanda fiye da mutane 400,000 suka gani.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel