Bidiyon Dogarin Sarauniya Elizabeth II Ya Yanke Jiki Ya Fadi Yayin Gadin Akwatin Gawarta

Bidiyon Dogarin Sarauniya Elizabeth II Ya Yanke Jiki Ya Fadi Yayin Gadin Akwatin Gawarta

  • Daya daga cikin dagorai da suke gadin akwatin gawar sarauniya Elizabeth II a dakin taro na Westminster ya yanke jiki ya fadi sumame
  • Bidiyon da aka wallafa ya nuna dogarin yana fadi kasa kafin wasu yan sanda biyu suka tafi suka tallafa masa
  • Dogarin ya fadi ne yayin da aake fitar da akwatin gawar sarauniyar daga cocin St Giles a Edinburgh kuma mutane suna ta tsokaci kan bidiyon

Wani dagorin fadar gidan sarautan Birtaniya ya yanke jiki ya fadi a kan mimbari inda ya ke gadin akwatin gawar sarauniya Elizabeth ta II.

Dogarin Sarauniya
Dogarin Sarauniya Elizabeth II Ya Yanke Jiki Ya Fadi Yayin Gadin Gawarta. Hoto: Mirror.
Asali: UGC

A cewar Mirror, yan sanda sun garzaya sun taimaka masa bayan ya fadi kasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Aka Fallasa Wata Budurwa Da Ke Bara Da Jinjirin Karya A Lagas

Mutane da dama sun yi layi a titunan Landan domin ganin gawar sarauniyar da ke dakin taro na Westminster gabanin birne ta a ranar Litinin 19 ga watan Satumba.

Sojoji sun yi fareti da akwatin gawar daga fadar Buckingham a ranar Laraba, 14 ga watan Satumba.

Bisa, alamu daya daga cikin dogarin ya gaza jurewa hakan yasa ya fadi sumamme.

Mutane masu zaman makoki sun yi mamaki a lokacin da ya fadi kasa kamar yadda bidiyon ya nuna.

Ya faru ne a lokacin da dogaran ke shirin sauya aiki amma daya cikinsu ya yanke jiki ya fadi.

An ga yan sanda biyu sun tafi su taimaka masa kafin bidiyon ya yanke sannan sai aka fara nuna hotunan majalisun Birtaniya.

Mutane da dama suna ta tofa albarkacin bakinsu kan bidiyon inda wasu ke cewa juyayin rasuwar Sarauniyar ne ya kidima shi.

Kalli bidiyon:

Farfesa Yar Najeriya Da Ta Yi Wa Sarauniyar Ingila Fatar Mummunan Mutuwa Ta Bayyana Ainihin Dalilinta

Kara karanta wannan

Yadda Jikan Sarauniya Elizabeth II Ya Gaji Tamfatsetsen Gidanta Mai Darajar N426b

A wani rahoton, Farfesa Uju Anya ta bayyana dalilin da yasa ta furta marasa dadi game da sarauniyar Ingila, Elizabeth ta II a yayin da ta ke gadon mutuwa.

Farfesan, haifafiyar Najeriya wacce ke nazari a bangaren harsuna da yanayin rayuwar al'umma ta janyo cece-kuce a Twitter kan zolayar sarauniyar ta Ingila.

Anya ta yi rubutu a shafinta na Twitter inda ya yi wa sarauniyar fatar mummunar mutuwa cikin ukuba.

Tuni dai Twitter ta cire rubutun domin ya saba dokoki da ka'idojin ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel