Farfesa Yar Najeriya Da Ta Yi Wa Sarauniyar Ingila Fatar Mummunan Mutuwa Ta Bayyana Ainihin Dalilinta

Farfesa Yar Najeriya Da Ta Yi Wa Sarauniyar Ingila Fatar Mummunan Mutuwa Ta Bayyana Ainihin Dalilinta

  • Farfesa Uju Anya ta bayyana dalilin da yasa ta furta kakkasan maganganu game da sarauniyar Ingila lokacin tana daf da rasuwa
  • Anya ta ce gwamnatin Birtaniya karkashin mulkin sarauniya Elizabeth ta II ta taimakawa Najeriya yayin yakin Biafra
  • Mai binciken wacce iyalanta suna cikin wadanda aka kashe a yakin, ta ce gwamnatin Birtaniya ta kashe rayuwa saboda abin da zata amfana da shi

Twitter - Farfesa Uju Anya ta bayyana dalilin da yasa ta furta marasa dadi game da sarauniyar Ingila, Elizabeth ta II a yayin da ta ke gadon mutuwa.

Farfesan, haifafiyar Najeriya wacce ke nazari a bangaren harsuna da yanayin rayuwar al'umma ta janyo cece-kuce a Twitter kan zolayar sarauniyar ta Ingila.

Uju Anya
Farfesa Yar Najeriya Da Ta Yi Wa Sarauniyar Ingila Fatar Mummunan Mutuwa Ta Bayyana Ainihin Dalilinta. Hoto: @UjuAnya.
Asali: Twitter

Anya ta yi rubutu a shafinta na Twitter inda ya yi wa sarauniyar fatar mummunar mutuwa cikin ukuba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tuni dai Twitter ta cire rubutun domin ya saba dokokinta.

Yar jarida Marcir Cipriani ta tuntubi Anya

Marcie Cipriani, mai gabatar da shirya-shirye a talabijin a Amurka, ta tuntubi Farfesa Anya domin gano dalilin da yasa ta furta maganganun game da sarauniya.

Da ta ke mayar da martani, Farfesa Anya ta rubuta:

"Iyaye na da yan uwa na suna cikin wadanda aka kashe yan uwansu. Daga 1967 zuwa 1970, an kashe fararen hula fiye da miliyan 3 lokacin da mutanen Igbo suka yi yunkurin neman yanci su kafa Biafra.
"Yan uwa na suna cikin wadanda aka kashe. An haife ni bayan kammala wannan kisan kare dangin, wanda gwamnatin Birtaniya karkashin Sarauniya Elizabeth II ta taimaka aka yi.

Ta cigaba da cewa:

"An yi tallafin ta hanyar siyasa, makamai, bama-bamai, jirage, motoccin sojoji da kayayyaki da gwamnatin Birtaniya ta bada a kashe mu don kare abin da take zamu daga arzikin man fetur a yankin mu.

"Mutane ne na sun jure mummunan wahala, wanda har yanzu yana shafar rayuwar mu, domin har yanzu muna jimamin rashin da muka yi kuma muna kokarin sake gina abin da aka lalata mana.
"Abubuwan da muke tattaunawa a yanzu sun hada da mutane da aka rasa, wadanda suka rasa muhalli, inda mutane suka yi hijira, inda aka birne gawarwaki. Ba su kunshi maganganu masu sanyaya zuciya da girmamawa ga wadanda suka kashe yan uwansu suka lalata rayuwar mu."

Sarauniya Elizabeth Ta II: Abubuwa 5 Da Za Su Faru Yanzu Bayan Mutuwar Sarauniyar Mafi Dadewa Kan Mulki Read

A wani rahoton kun ji cewa kafin sanarwar rasuwarta, mutane a fadin duniya sun shiga yanayin damuwa bayan da fadar Buckingham ta sanar cewa likitoci na duba Sarauniya Elizabeth ta II a Scotland.

Wasu da dama kuma sun ce sanarwar da fadar gidan sarauntan na Birtaniya ya fitar, wacce ya ce likitoci sun damu da halin da ta ke ciki ya nuna rashin lafiyar ya yi tsanani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel