Twitter Ta Dau Zafi Bayan Dan Amurka Ya Yi Wa Ministan Buhari Izgili, Ya Kira Shi 'Mr Mugu'

Twitter Ta Dau Zafi Bayan Dan Amurka Ya Yi Wa Ministan Buhari Izgili, Ya Kira Shi 'Mr Mugu'

  • Cacan baki ya kaure tsakanin Festus Keyamo, karamin ministan kwadago na Najeriya, da wani baamurk, Jeffrey Guterman a shafin Twitter
  • Mai magana da yawun kungiyar kamfen din na Asiwaju Bola Tinubu ya bukaci Guterman ya dena saki baki a siyasar Najeriya shi kuma Guterman ya kira shi 'Mugu'
  • Yan Najeriya da dama sun yi ta tsokaci kan musayar maganganun da Keyamo da Guterman suka yi a shafin Twitter

Twitter - Dr Jeffery Guterman, tsohon likitan masu matsalar kwakwalwa a Amurka ya tada kura a Twittan Najeriya, a ranar Talata, bayan kiran Festus, Keyamo, karamin ministan Kwadago da Samar da Ayyuka kuma kakakin kamfen din dan takarar shugaban kasa na APC, 'Mr Mugu'.

Mugu kalma ce da ake amfani da ita a harshen pidgin ga mutum mara basira.

Kara karanta wannan

Tashin hankali ga 'yan Najeriya yayin da Buhari yace zai haramta amfani da kananzir

Guterman
Twitter Ta Dau Zafi Bayan Dan Amurka Ya Yi Wa Ministan Buhari Izgili, Ya Kira Shi 'Mr Mugu'. Hoto: @JeffreyGuterman
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Guterman ya yi martani ne kan sharhin da Keyamo ya yi kan bidiyon Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na LP, inda ya bukaci wani cikin hafimansa ya karanta sakon na sukar takararsa.

Ya rubuta:

"Ka ji kunya Festus Keyamo."

A martaninsa, ministan ya bukaci baamurken ya dena saka baki a siyasar Najeriya.

"@JeffreyGuterman, sojan haya mara katin zabe na Najeriya (PVC), ina baka shawarar ka dena shiga batun siyasar cikin gida na Najeriya. Hukumomin da na ke aiki da su ba za su bari in ragargaje ka ba."

Daga nan Guterman ya mayar da martani mai zafi.

Ya rubuta:

"Ba zan dena saka baki a siyasar Najeriya ba, Mr Mugu @fkeyamo. #PeterObiForPresident."

A bangare guda, yan Najeriya a Twitter sun rika tofa albarkacin bakinsu kan batun, ga wasu daga cikinsu.

Kara karanta wannan

Atiku ya sha alwashin yin abin da Buhari ya gaza idan aka zabe shi a 2023

@chukwuebuker ya rubuta:

"Kada ka damu da Babban Kare Shirme; abin kunya ne gare mu baki daya. Mun gode @JeffreyGuterman bisa abin da ka ke yi."

@Nemonwa:

"Ni Mr Mugu ne ya birge ni, Kada ka damu da Mugun da ke ikirarin SAN."

@LuqmanTI_2:

"Jeffrey nan gaba ka kira shi babban mai kare shirme."

Lokacin da 'Mr Mugu' ya fara karade Twitter, Guterman ya wallafa hoton sikirin ya rubuta, 'ku cigaba da watsawa'.

Dangi da 'yan uwa na saka 'yan siyasa satar kuɗin gwamnati, Ministan Buhari

A wani labarin daban, karamin ministan Kwadago da Samar da Ayyuka, Festus Keyamo SAN, ya ce matsin lamba da yan uwa da abokai ke yi wa mutane da ke rike da mulki ne neman su basu kudi ne ka karfafa musu gwiwa suna sata da aikata rashawa.

A cewar The Sun, Keyamo ya yi wannan furucin ne yayin jawabin da ya yi a ranar Laraba a Abuja yayin kaddamar da shirin 'Corruption Tori Season 2' da Signature TV da gidauniyar MacArthur suke daukan nauyi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel