Dangi da 'yan uwa na saka 'yan siyasa satar kuɗin gwamnati, Ministan Buhari

Dangi da 'yan uwa na saka 'yan siyasa satar kuɗin gwamnati, Ministan Buhari

  • Festus Keyamo, SAN, ministan kwadago na Nigeria ya ce yan uwa da abokai ke saka masu rike mulki sata saboda takura musu da rokon kudi
  • Ministan ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da wani shirin yaki da rashawa da ake watsawa a kafafen watsa labarai mai suna 'Corruption Tori'
  • A bangarensa, Farfesa Bolaji Owasanoye SAN, shugaban hukumar yaki da rashawa ta ICPC ya bukaci dukkan yan Nigeria su bada gudunmawa don yaki da rashawar

Ministan Kwadago da Samar da Ayyuka, Festus Keyamo SAN, ya ce matsin lamba da yan uwa da abokai ke yi wa mutane da ke rike da mulki ne neman su basu kudi ne ka karfafa musu gwiwa suna sata da aikata rashawa.

A cewar The Sun, Keyamo ya yi wannan furucin ne yayin jawabin da ya yi a ranar Laraba a Abuja yayin kaddamar da shirin 'Corruption Tori Season 2' da Signature TV da gidauniyar MacArthur suke daukan nauyi.

Ministan Kwadago da Samar da Ayyukan yi, Festus Keyamo
Ministan Kwadago da Samar da Ayyukan yi, Festus Keyamo, SAN. Hoto: The Nigeria Lawyers
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: An fara amfani da 'tsafi' domin hana ƴan bindiga kai wa ƴan sanda hari a kudu maso gabas

An kirkiri shirin ne domin wayar da kan mutane game da rawar da za su iya takawa wurin yaki da rashawa da cin hanci a Nigeria ta hanyar amfani da harsunan mutanen Nigeria.

Minsitan ya shawarci yan Nigeria su bada gudunmawa wurin yaki da rashawar da ya ce ta zama cuta da ke lalata al'umma kuma ya zama dole a kawar da ita idan ana son cigaba.

Dalilin kirkirar shirin na yaki da rashawa

Farfesa Bolaji Owasanoye SAN, shugaban hukumar yaki da rashawa ta ICPC, shima ya yi jawabi yayin taron kaddamar da shirin yaki da rashawar inda ya lissafa wasu dalilan da yasa aka kirkiri shirin.

KU KARANTA: Da Duminsa: Allah ya yi wa jigo a jam'iyyar APC rasuwa a Zamfara

Ya ce:

"Rashawa barazana ce ga tsaron kasa. Barazana ce ga halayen zamantakewa da al'adun mu da tattalin arziki da siyasa. Abin da ya dace shine kowa ya bada gudunmawa wurin karfafa yaki da rashawa kamar Signature TV.
"Muna bukatan karin mutane su shigo a yi wannan yaki da rashawar tare da su. Mu a bangaren mu na ICPC mun kasance muna bullo da shirye-shirye da tsare-tsare da suka bamu damar cin nasarori wurin rage rashawa a Nigeria."

Charles Soludo, tsohon gwamnan CBN ya zama dan takarar gwamnan APGA

A wani labarin daban, Charles Soludo, tsohon gwamnan babban bankin Nigeria, CBN, ya lashe zaben fidda gwani na kujerar gwamna a jam'iyyar All Progressives Grand Alliance, APGA.

A cewar Daily Trust, Soludo ya samu kuri'u 740 inda ya doke Ezenwanko Christopher da ya samu kuri'u 41, ThankGod Ibe da ya samu kuri'u 4 da Okolo Chibuzor wanda ya samu kuri'u bakwai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel