Bam Ya Fashe a Masallacin Herat Na Afghanistan, Fitaccen Limami Ya Rasu

Bam Ya Fashe a Masallacin Herat Na Afghanistan, Fitaccen Limami Ya Rasu

  • Yanzu muke samun labarin mutuwar wani fitaccen malamin addinin Islama a kasar Afghanistan
  • Bam ya tashi a wani masallaci, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, gwamnatin kasar ta magantu
  • Ana yawan samun hare-haren bama-bamai a Afghnanistan cikin kwanakin nan, IS ke daukar alhakin harin

Herat, Afghanistan - An samu fashewar bam a daya daga cikin manyan masallatan yammacin Afganistan a ranar Juma'a, inda aka rasa wani babban limami.

Limamin dai shi ne ya yi da'awar kashe duk wani da ya yi inkari da manufofin gwamnatin Taliban a farkon wannan shekara, rahoton The Guardian.

Hotunan da aka ta yadawa a Twitter sun nuna jini kaca-kaca a masallacin na Gazargah da ke birnin Herat. Kafofin yada labaran kasar shaida cewa, ana fargabar mutane da dama sun rasa rayukansu.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: Wani abu zai faru, gwamnati ya share ASUU, ta kira ganawa da shugabannin jami'o'i

Bam ya tashi a masallaci, limami sananne ya rasu
Bam ya fashe a masallacin Herat na Afghanistan, fitaccen limami ya rasu | Hoto: STR/AFP
Asali: UGC

An rage samun tashe-tashen hankula a Afghanistan tun bayan da kungiyar Taliban ta karbe mulki bara, sai dai akan yawan samun tashin bama-bamai a kasar cikin 'yan watannin nan. Kungiyar ta'addanci ta IS ce amsa kitsa dukkan hare-haren.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwamnatin Taliban ta yi magana

Kakakin gwamnatin Taliban, Zabihullah Mujahid ya tabbatar da mutuwar Mujib ur Rahman Ansari a harin na ranar Juma'a.

A cewar Mujahid ta shafin Twitter:

"Bujumin malamin addini mai tsananin kwarjini na kasar nan ya yi shahada a wani mummunan hari."

Hakazalika, ya bayyana ta'aziyyarsa ga iyalai da dangin malamin da kasar ke matukar ji dashi ko koyarwarsa.

Ansari dai fitaccen malami ne mai fada a ji a Afghanistan, kuma ya shahara da fadin zafafan kalamai masu jawo cece-kuce.

An harbe mahalarta daurin aure a Afghanistan saboda sun saurari wake-wake

Kara karanta wannan

Daga karshe: Osinbajo ya shiga batun ASUU, ya fadi abin da gwamnati za ta yi

A wani labarin, akalla mutane biyu da suka halarci wani daurin aure a gabashin kasar Afghanistan aka kashe a ranar Juma’a, 29 ga watan Nuwamba, 2021.

CNN ta fitar da rahoto a makon nan, tace an kashe wadannan Bayin Allah ne saboda sun saurari waka.

Ana zargin wasu ‘yan kungiyar Taliban da wannan aika-aika, inda suka budawa masu halartar wannan biki wuta. Hakan ya yi sanadiyyar rasa Bayin Allah.

Asali: Legit.ng

Online view pixel