Gwamnatin Buhari Ta Nemi Ganawa da Shugabannin Jami’o’i Don Warware Yajin ASUU

Gwamnatin Buhari Ta Nemi Ganawa da Shugabannin Jami’o’i Don Warware Yajin ASUU

  • Yayin da malaman jami'o'i ke ci gaba da zaman yajin aiki, gwamnati na kokarin kawo mafita ga yajin
  • Ministan ilimi na Najeriya, Adamu Adamu ya kira shugabannin jami'o'i domin warware damuwar ASUU
  • Akalla kwanaki 199 malaman jami'a suka shafe cikin yajin aikin, lamarin da yasa dalibai ke zaman kashe wando

FCT, Abuja - A ci gaba da neman mafita ga yajin aikin ASUU, ministan Ilimi na Najeriya, Adamu Adamu, ya kira dukkan shugabannin jami'o'in tarayya na kasar domin wata tattaunawa.

Sanarwar ta fito ne ta hannun hukumomin jami’o’in da abin ya shafa a ranar 26 ga watan Agusta, dauke da sa hannun mataimakin babban sakataren gudanarwar NUC Chris Maiyaki.

Rahoton Premium Times ya ce za ayi taron ne a ranar 6 ga watan Satumba kuma zai mai da hankali ne ga shawarwarin da aka cimma da malaman jami’o’in da ke yajin aiki a yanzu, da dai sauran batutuwa.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Osinbajo ya shiga batun ASUU, ya fadi abin da gwamnati za ta yi

Adamu Adamu ya nemi ganin shugabannin jami'o'in tarayya
Gwamnatin Buhari ta nemi ganawa da shugabannin jami'o'i don warware yajin ASUU | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Idan baku manta ba, kungiyar malaman jami'a ta ASUU ta shiga yajin aiki a ranar 14 ga watan Fabrairu saboda wasu matsaloli da suka shafi jin dadin aiki.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bayan doguwar tattaunawa, kungiyoyin SSANU da NASU sun ayyana janye yajin da su ma suke ciki a makon jiya bayan cimma matsaya da gwamnatin Buhari.

A wannan karon, ganawar ta NUC da shugabannin jami'o'in tarayya zai dukufa ne ga warware rikicin yajin aikin da kuma cimma matsaya kan yadda za a shawo kan lamarin cikin sauki, rahoton Tribune Online.

A baya, shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ya ce babu gudu babu ja da baya har sai gwamnati ta amince da bukatun kungiyar kafin a bude jami'o'i.

Ya Kamata Mu Sa Baki Domin Warware Matsalolin Najeriya, Osinbajo Ga Gwamnonin APC

A wani labarin, yayin da yajin aikin ASUU ya kara ta'azzara, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ce to yanzu kam ya kamata na himmatuwa don warware matsalolin Najeriya baki daya.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: ASUU ta gama tattaunawa a Abuja, ta sake fitar da matsaya

An ruwaito Osinbajo na fadin haka ne a yau Talata 30 ga watan Agusta yayin da gwamnonin APC suka kai masa ziyarar sannu bayan murmurewarsa daga rashin lafiya, TheCable ta kawo.

Idan baku manta ba, an yiwa Osinbajo tiyata a gwiwarsa a kwanakin baya, lamarin da yasa ya tafi hutu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel