Bayan kwashe shekara 3 yana tattaki, 'dan kasar Afrika ta kudu ya isa Saudiyya don sauke farali

Bayan kwashe shekara 3 yana tattaki, 'dan kasar Afrika ta kudu ya isa Saudiyya don sauke farali

  • Wani mutum'dan kasar Afirka ta kudu, wanda ke zaune a Cape Town ya isa Makkah bayan daukar shekaru uku yana tafiya a kafa
  • An ruwaito yadda mutumin ya fara tafiya tun ranar 30 ga watan Agustan 2018, inda ya keta kasashe 6 dokar kullen Korana ta dakatar dashi a Palestine
  • Bayan bude iyakar kasar, mutumin ya cigaba da tafiyar da ta ya kai sama da shekara 1 zuwa garin Makkah
  • Haka zalika, yayin zantawa da manema labarai a kan kalubalen da ya fuskanta, mutumin ya dauki alwashin komawa gida a kafa kamar yadda ya zo

Bayan shekaru uku da kama hanya daga gidansa zuwa kasa mai tsarki ta Musulunci, Saheed, wani 'dan Afirka ta kudu ya kafa tarihin isa Makkah a kafa.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Kotu ta daure janar din soja na bogi shekaru 7 a magarkama

Kamar yadda rahoton ya bayyana, mutumin ya keta kasashen Afirka da Turai da dama kafin ya isa inda ya yi niyya, jaridar The Islamic Information ta ruwaito.

South African
Bayan kwashe shekara 3 yana tattaki, 'dan kasar Afrika ta kudu ya isa Saudiyya don sauke farali. Hoto daga theislamicinformation.com
Asali: UGC

Bayan ya fara tafiyarsa a ranar 30 ga watan Agusta, 2018, ya bi ta Zimbabwe, Tanzania, Kenya, Sudan, Misira da Palestine, inda dokar kullen Korona ta tilasta masa dakata wa.

Sanadiyyar sake bude iyakar, mutumin ya cigaba da tafiya ta Jordan, Madina, da Makkah kafin ya isa Makkah bayan daukar sama da shekara daya a Palestine.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mutumin mazaunin Cape Town, Saheed, ya ce zai sake takawa da kafafunsa zuwa gida bayan ya kammala aikin Hajji.

Jim kadan bayan isa Saudi Arabiya, ya zanta da manema labarai a kan kalubalen da ya fuskanta.

An Tiso Keyar Maniyattan Kano 7 Daga Saudiyya Zuwa Najeriya Saboda Biza Ta Bogi

Kara karanta wannan

Ragon layya N300K: Dillalai sun yi tagumi, jama'a ba sa zuwa sayen raguna

A wani labari na daban, an dawo da wasu maniyyata yan jihar Kano gidajensu bayan sun tafi Jidda a ranar Alhamis saboda biza da suke da shi na bogi ne, rahoton Daily Trust.

Biyar cikin maniyattan sun tafi Saudiyya ne ta hannun kamfanonin jiragen yawo yayin da biyu cikinsu kuma ta hannun Hukumar Alhazai na Jihar Kano suka tafi.

Daya cikin wadanda aka dawo da su, Dahiru Yau Musa, ya ce ya samu bizansa ne ta hannun Quraish Travel Agency, yayin da sauran hudun suka samu nasu ta hannun Mafimishkila Travel and Tours, Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng