An Tiso Keyar Maniyattan Kano 7 Daga Saudiyya Zuwa Najeriya Saboda Biza Ta Bogi

An Tiso Keyar Maniyattan Kano 7 Daga Saudiyya Zuwa Najeriya Saboda Biza Ta Bogi

  • Mahukunta a kasar Saudiyya sun dawo da wasu maniyattan Najeriya bakwai da aka gano biza na bogi suka tafi
  • Biyar daga ciki maniyyatan sun tafi kasar mai tsarki ne ta jiragen yawo yayin da biyu cikinsu sun tafi ne karkashin hukumar alhazai ta Kano
  • Alhaji Muhammad Abba Danbatta, Sakataren Hukumar Alhazai ta Kano ya ce wani ma'aikacinsu ne ya yaudari mutanen biyu ya kutsa sunansu cikin jerin alhazai

An dawo da wasu maniyyata yan jihar Kano gidajensu bayan sun tafi Jidda a ranar Alhamis saboda biza da suke da shi na bogi ne, rahoton Daily Trust.

Biyar cikin maniyattan sun tafi Saudiyya ne ta hannun kamfanonin jiragen yawo yayin da biyu cikinsu kuma ta hannun Hukumar Alhazai na Jihar Kano suka tafi.

Maniyatta
An Fatattako Maniyattan Kano 7 Daga Saudiyya Kan Biza Na Bogi. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Daya cikin wadanda aka dawo da su, Dahiru Yau Musa, ya ce ya samu bizansa ne ta hannun Quraish Travel Agency, yayin da sauran hudun suka samu nasu ta hannun Mafimishkila Travel and Tours, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Hajj 2022: Yadda alhazan Najeriya da na duniya su ka yi cincirindo a Dutsen Arfah

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce ba su san biza na bogi aka basu ba sai da suka isa Filin Saukan Jirage na Sarki Abdulazeez.

"Muna layi da sauran maniyyata da aka zo kaina, suna bukaci in tsaya a gefe. Bayan an kammala tantance sauran ne suka fada mana bizan mu na bogi ne.
"Sunyi magana da jami'an NAHCON. Sunyi kokarin daidaita lamarin amma bai yiwu ba. A karshe, an fada mana za a dawo da mu Najeriya. Sauran ya zama tarihi yanzu," ya bayyana.

Dahiru ya ce abin ba dadi a matsayin musulmi ya shiga kasa mai tsarki kuma a dawo da shi, ya kuma sha alwashin zai tafi kotu.

"Tun bayan dawowa na, jami'in hukumar jigilar jiragen ya nemi mu hadu amma na ki, bana son jin wani abu sai mun hadu a kotu.
"Kuma zan yi korafi ofishin jakadancin Saudiyya a nan don su wanke ni saboda tafiya a gaba," ya kara da cewa.

Kara karanta wannan

Fashin magarkamar Kuje: FG ta fitar da bayanan 'yan Boko Haram din da suka tsere

Martanin Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Kano

Da ya ke tabbatar da lamarin, Sakataren Hukumar Alhazai na Kano, Alhaji Muhammad Abba Danbatta, ya ce maniyattan biyu daga kora ba daga hukumar suke ba, wani ma'aikaci ne ya shigar da su ta bayan gida.

"Da na ji labarin misalin karfe 2 na dare. Na garzaya zuwa filin jirgi na gana da maniyattan biyu mace da miji da suka yi ikirarin daga cibiyar mu da Sumaila suke.
"Na jira jami'in mu na Sumaila ya ce bai san su ba kuma ba su san shi ba. Bincike ya nuna wani ma'aikacin, Abdurrahman, ne ya yaudare su. Ya basu biza ta bogi da rasit," in ji shi.

Danbatta ya ce an kai rahoto ga hukumomin da suka dace kuma zai fuskanci hukuncin da doka ta tanada.

Mawaki Sufin Zamani Zai Saki Bidiyo Da Murya Na Neman Afuwar Matan Kannywood

A wani rahoton, jami'an hukumar yan sandan farin kaya, DSS, sun kama mawakin Hausa, Sarfilu Umar Zarewa wanda aka fi sani da Sufin Zamani, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Harin Kuje: Kun Bani Kunya, Buhari Ya Fada Wa Hukumomin Tattara Bayanan Sirri

Kungiyar masu fina-finai ta MOPPAN ce ta yi korafi kansa saboda wata waka da ya yi mai suna "Matan Fim Ba Su Zaman Aure."

Matan Kannywood ba su ji dadin wakar da Sufin Zamanin ya yi ba inda suka ce cin mutunci ne a gare su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel