Allah ya yi: Daga karshe dai an samo hanyar magance HIV, wata mata ta warke sarai

Allah ya yi: Daga karshe dai an samo hanyar magance HIV, wata mata ta warke sarai

  • Gamayyar wasu masana kimiyya sun samar da hanyar magance cutar kanjamau a kasar Amurka a yanzu
  • Rahoton da kafafen yada labarai na waje suka fitar ya bayyana cewa, an samu matar da ta warke sarai daga kanjamau
  • Sai dai, a wasu lokuta a 2009 da 2019 an samu wasu mutanen da suka warke daga cutar, ta wata hanyar daban

Kasar Amurka - Wata mata da ake kira da ‘Majinyaciyar New York’ domin sakaya sunanta, an ba da rahoton cewa ta zama mace ta farko da ta warke sarai daga cutar kanjamau, TheCable ta tattaro.

An ce an sanar da wannan ci gaban ne a ranar Talata 15 ga watan Fabrairu a wani taro kan cututtuka mai taken: ‘Conference on Retroviruses and Opportunistic Infections’, wanda aka gudanar ta yanar gizo.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun farmaki sabuwar kasuwar shanu a jihar Abia, sun kashe mutane da dama

Cutar karya garkuwar jiki ta kanjamau ta kusa zuwa karsge
Allah ya yi: Daga karshe dai an samo hanyar magance HIV, wata mata ta warke sarai | Hoto: nytimes.com
Asali: UGC

A cewar kafar labarai ta NBC, majinyaciyar ta sami magani ne a Cibiyar Kiwon Lafiya ta New York-Presbyterian Weill Cornell a kasar Amurka.

An ce ta kamu da cutar kanjamau a 2013, yayin da aka tabbatar da cewa tana dauke da cutar sankarar bargo a 2017.

Ya lamarin yake?

Hadin maganin, wanda aka ce ya kunshi amfani da jinin da aka dauko daga igiyar cibiya, ya mai da hankali ne ga inganta garkuwar jiki.

Hakazalika, rahoton ya ce, an yi amfani da tsarin jinya na haplo-cord transplant, wanda aka samar don fadada damar samar da maganin ciwon daji ga mutanen da ke da cutar jini.

A cewar jaridar New York Times, duk da cewa masu bincike sun ce suna ci gaba da sanya ido kan yadda ake samun murmurewa daga cutar, amma a cikin watanni 14 da suka gabata ba a gano matar tana dauke da cutar kanjamau ba.

Kara karanta wannan

Tsohon kwamishinan Zamfara Danmaliki ya koka, ya ce ana barazana ga rayuwarsa

Jinyar ta ya zama mai mahimmanci idan aka yi la'akari da cewa mata sun fi yawa daga cikin mutanen da ke dauke da cutar kanjamau a duniya.

Bisa kididdigar da hadin gwiwar shirin Majalisar Dinkin Duniya kan cutar kanjamau (UNAIDS) ta fitar a 2021, “kashi 53 na dukkan mutanen da ke dauke da cutar kanjamau mata ne da yara mata”.

A baya, kafin wannan sabon ci gaba, an ce wasu maza biyu sun warke sarai daga cutar kanjamau a 2009 da 2019, ta hanyar yi musu dashen bargo.

Ranar Kanjamau ta Duniya: Mutum 35,000 na fama da cutar a jihar Kano, Gwamnatin Ganduje

A wani labarin, Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa akalla mutum 35,000 ke jinyar cutar Kanjamau a jihar yanzu haka.

Kwamishanan lafiyan jihar, Dr. Aminu Tsanyawa, ya bayyana hakan ne a hira da manema labarai a taron zagayowar ranar Kanjamau na duniya ranar Laraba, rahoton Daily Nigerian.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: An kashe yan ta’adda da dama yayin da sojoji suka farmaki mafakarsu a Yobe

A cewarsa, Gwamnatin jihar ke kula da dukkan masu fama da cutar. Dr. Aminu Tsanyawa ya bayyana cewa ana tattara bayanan masu cutar ne domin takaita yaduwar cutar a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel