Ranar Kanjamau ta Duniya: Mutum 35,000 na fama da cutar a jihar Kano, Gwamnatin Ganduje

Ranar Kanjamau ta Duniya: Mutum 35,000 na fama da cutar a jihar Kano, Gwamnatin Ganduje

  • An yi tarukan zagayowar ranar wayar da kan jama'a kan cutar Kanjamau a Duniya yau Laraba
  • Gwamnatin jihar Kano ta bayyana irin kokarin da take yi wajen rage yaduwar cutar a fadin jihar
  • Cutar Kanjamau na daga cikin cututtukan da har yanzu ba'a samu maganinsu ba

Kano - Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa akalla mutum 35,000 ke jinyar cutar Kanjamau a jihar yanzu haka.

Kwamishanan lafiyan jihar, Dr. Aminu Tsanyawa, ya bayyana hakan ne a hira da manema labarai a taron zagayowar ranar Kanjamau na duniya ranar Laraba, rahoton Daily Nigerian.

A cewarsa, Gwamnatin jihar ke kula da dukkan masu fama da cutar.

Dr. Aminu Tsanyawa ya bayyana cewa ana tattara bayanan masu cutar ne domin takaita yaduwar cutar a jihar.

Ya kara da cewa gwamnatin ta kafa cibiyoyi 600 a fadin jihar don tabbatar da iyaye mata masu cutar basu cinnawa jariransu ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ƴan ta'addan ISWAP sun sace ma'aikatan gwamnatin Jihar Borno

Ranar Kanjamau ta Duniya
Ranar Kanjamau ta Duniya: Mutum 35,000 na fama da cutar a jihar Kano, Gwamnatin Ganduje
Asali: UGC

'Yan Sanda Sun Kama Mutumin Da Ya Shafawa Mata 14 Cutar Ƙanjamau a Legas

A wani labarin kuwa, yan sanda sun kama wani Bolaniran Orimolade, mutumin da ya shafawa matarsa da yar ta da wasu mata da dama cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV/AIDS a jihar Legas, SaharaReporters ta ruwaito.

Ebenezer Omejalile, babban jami'in kungiyar kare hakkin yara da mutane marasa galihu ta Advocates for Children and Vulnerable Peoples Network ne ya sanar da hakan.

A cewar Omejalile, wanda ake zargin da aka fi sani da Bola Bebo, wanda ke ikirarin shi shugaban tashar mota na Iyana Iba ne ya dade yana cika bakin cewa babu wanda ya isa ya kama shi.

SaharaReporters ta ruwaito cewa Omejalile ya ce baya da matarsa da yarsa, ya kuma shafawa wasu mata 12 cutar da HIV ga gangan.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Allah ya yiwa Wazirin masarautar Hadejia rasuwa

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel