Zargin kona Al-Kur'ani: Fusatattun jama'a sun babbaka wani mutum a Pakistan

Zargin kona Al-Kur'ani: Fusatattun jama'a sun babbaka wani mutum a Pakistan

  • Fusatattun jama'a sun lakadawa wani mutum mugun duka tare kone shi a kasar Pakistan kan zarginsa da suke da kone shafukan Al-Qur'ani
  • Mummunan lamarin ya auku ne a daren Asabar a garin Khanewal da ke lardin Punjab a kasar Pakistan
  • An gano cewa firayim minista ya bukaci a cafko duk wadanda ke da hannu a kisan tare da 'yan sanda da suka kasa katabus a yayin da abun ke faruwa

Pakistan - Fusatattun jama'a sun kashe wani bawan Allah da ake zargi da kone Al-Qur'ani mai girma a kasar Pakistan.

An gano cewa jama'an sun lakada masa mugun duka tare da kona shi a garin mai suna Khanewal da ke lardin Punjab a kasar Pakistan, Aminiya Daily Trust ta wallafa.

Kara karanta wannan

Jonathan: Asalin abin da ya sa na kirkiro makarantun Almajirai a Arewa a mulkina

Jama'a masu yawa ne a halin yanzu aka tabbatar da an kama su sakamakon hannunsu a kisan. Lamarin ya auku a ranar Asabar, kamar yadda Firayim minsitan kasar na harkokin addini, Tahir Ashrafi ya sanar.

Zargin kona Al-Kur'ani: Fusatattun jama'a sun babbaka wani mutum a Pakistan
Zargin kona Al-Kur'ani: Fusatattun jama'a sun babbaka wani mutum a Pakistan. Hoto daga aminiya.dailytrust.com
Asali: UGC

Hakazalika, jami'an tsaro suna can suna cigaba da farautar sauran wadanda ke da hannu a kisan mutumin, Aminiya Daily Trust ta ruwaito.

Jami'an 'yan sanda a lardin sun ce a kalla an yi ram da mutum 15 da ke da hannu a cikin kisan kuma ana cigaba da farautar kusan tamanin da biyar.

Firayim ministan kasa, Imran Khan, ya bayar da umarni daukar tsatsauran mataki kan duk wanda ke da hannu a cikin barnar, daga ciki har da jami'an 'yan sandan da lamarin ya auku a kan idanunsu amma suka kasa yin komai.

Kara karanta wannan

Tarihi a 2022: Manya-manyan laifukan kashe-kashen tsafi 4 da suka girgiza 'yan Najeriya

"Za mu dauka mataki mai tsauri a kan wannan lamarin kuma za mu tabbatar da cewa doka ta yi halin ta. Ba zai yuwu mu kyale mutane su dinga daukar doka a hannunsu ba," cewar firayim ministan a wata muhimmiyar sanarwa.

Wannan kisan na zuwa ne kusan bayan wata 2 da aka nada wa wani manajan masana'anta dan kasar Sri Lanka mugun duka har ya mutu saboda zarginsa da aikata batanci.

Jama'ar sun tattaru ne a wani Masallaci a daren Asabar bayan dan wani limamin ya sanar da cewa ya ga wanda ake zargin ya na babbaka wasu shafukan Al-Qur'ani, a cewar Munawar Hussain, jami'in dan sanda da ke yankin.

A cewarsa, bayan 'yan sanda sun isa wurin, sun riski mutumin daddaure a jikin bishiya ba ya iya ko motsawa. Ya ce sun kansu 'yan sanda sai da jama'ar suka kai musu farmaki.

Fusatattun matasa sun kurmushe mutum 5 da ake zargin 'yan bindiga ne a Edo

Kara karanta wannan

Mun shiga uku: Tsadar man fetur ya sa 'yan Najeriya kuka, sunyi zazzafan martani

A wani labari na daban, a ranar Lahadi da ta gabata ne wasu fusatattun matasa suka bankawa wasu mutum 5 da ake zargin da garkuwa da mutane wuta a kan babbar hanyar Afuze-Ukoha dake karamar hukumar Owan ta yamma a jihar Edo.

Kamar yadda TheCable ta ruwaito, wadanda ake zargin sun tare da sace wasu matafiya kan babbar hanya kuma sun kai su wani makusancin daji.

Amma kuma cike da sa'a ga matafiyan, masu garkuwa da mutanen sun shiga hannun 'yan sa kai wadanda suka fito dasu daga dajin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel