Fusatattun matasa sun kurmushe mutum 5 da ake zargin 'yan bindiga ne a Edo

Fusatattun matasa sun kurmushe mutum 5 da ake zargin 'yan bindiga ne a Edo

  • Fusatattun matasa a jihar Edo sun kone wasu mutum 5 har lahira wadanda ake zargi da garkuwa da mutane
  • Mutum 5 din sun tare matafiya a babbar hanya inda suka kwashesu zuwa wani daji dake Afuze-Ukoha a Edo
  • Tuni 'yan sa ka suka bi su tare da kama masu satar jama'an, amma matasa suka kwace su inda suka banka musu wuta

A ranar Lahadi da ta gabata ne wasu fusatattun matasa suka bankawa wasu mutum 5 da ake zargin da garkuwa da mutane wuta a kan babbar hanyar Afuze-Ukoha dake karamar hukumar Owan ta yamma a jihar Edo.

Kamar yadda TheCable ta ruwaito, wadanda ake zargin sun tare da sace wasu matafiya kan babbar hanya kuma sun kai su wani makusancin daji.

Amma kuma cike da sa'a ga matafiyan, masu garkuwa da mutanen sun shiga hannun 'yan sa kai wadanda suka fito dasu daga dajin.

KU KARANTA: Dubun Abdullahi Bummi shugaban 'yan bindigan Jigawa ta cika, an ceto tsohuwa 1

Kara karanta wannan

An yi luguden wuta tsakanin 'yan fasa-kwaurin shinkafar waje da jami'an kwastam

Fusatattun matasa sun kurmushe mutum 5 da ake zargin 'yan bindiga ne a Imo
Fusatattun matasa sun kurmushe mutum 5 da ake zargin 'yan bindiga ne a Imo. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Ku tarwatsa bangaren Yari na APC a Zamfara, Shinkafi yayi kira ga Buni da IGP

Kamar yadda Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya ya ruwaito, hango wadanda ake zargin ke da wuya, fusatattun matasan suka kwace miyagun inda suka banka musu wuta.

Wadanda ake zargin da garkuwa da mutanen sun kwashe matafiyan zuwa daji ba tare da sanin cewa 'yan sa kai na kusa ba kuma sun san abinda ke faruwa.

"Da yanzu masu garkuwa da mutanen sun fara tuntubar iyalan matafiyan domin karbar kudin fansa ba don sadaukantakar 'yan sa kan ba," wata majiya tace.

Bello Kontongs, mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Edo wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce ana cigaba da bincike.

"Bayan sace jama'an, 'yan sa kan sun shiga daji neman 'yan ta'addan wadanda aka kama a cikin daji," Kontongs yace.

“A yayin da suka fara fitowa zuwa yankin Uokha, a kan hanyarsu ta zuwa ofishin 'yan sanda fusatattun matasa suka tsaresu inda suka kwace su daga hannun 'yan sa kai. Duk kokarin 'yan sanda ya tashi a banza tunda sai da matasan suka konesu kurmus."

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Shugaban 'yan fashi ya kai hari kauyukan Zamfara, ya sace mutum 150 saboda an kama mahaifinsa

A wani labari na daban, Chukwuma Soludo, daya daga cikin 'yan takarar zaben gwamnonin da za a yi a jihar Anambra na ranar shida ga watan Nuwamban shekarar nan yace har yanzu yana cikin 'yan takara.

Daily Trust ta ruwaito cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, ta cire sunan shi daga cikin jerin 'yan takara.

A wata takarda da kungiyar yakin neman zabensa ta fitar a madadinsa, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya ya ce har yanzu shine dan takarar jam'iyyar APGA, Daily Trust ta wallafa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel