Innalillahi: An tumurmushe yarinya 'yar shekara 6 a filin buga wasan kofin nahiyar Afrika

Innalillahi: An tumurmushe yarinya 'yar shekara 6 a filin buga wasan kofin nahiyar Afrika

  • An samu cikas a filin wasan kwallon kafa a kasar Kamaru, inda aka take wata yarinya 'yar shekaru shida
  • Lamarin ya faru ne yayin da 'yan kallon ke tururuwan shiga filin wasan kwallon gabanin fara wasa a Yaounde
  • Shugaban kasa ya yi magana, ya bayyana rashin jin dadinsa ga lamarin, inda ya ba da umarnin bincike cikin gaggawa

Yaounde, Kamaru - An tabbatar da mutuwar wata yarinya ‘yar shekaru 6 a cikin mutane takwas da suka mutu a wani abin da aka bayyana a matsayin turmutsitsi da aka yi a wani filin wasa a Kamaru a gasar cin kofin nahiyar Afirka.

Kimanin mutane 50 ne suka jikkata tare da kwantar da wasu da dama a asibiti bayan da 'yan kallo suka kutsa kai cikin filin wasa na Olembe da ke Yaounde babban birnin Kamaru gabanin wasan da kasar za ta yi da Comoros a yammacin ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ana fargabar tankar mai ta kashe wasu mutane da dama a wani hadari

Filin wasan kwallo
Innalillahi: An tattake yarinya 'yar shekara 6 a filin buga wasan kofin nahiyar Afrika | Hoto: thecable.ng
Asali: Twitter

An samu rahotannin murkushe mutanen yayin da mutane ke shiga filin wasan, kamar yadda kafar yada labarai ta LSI Africa ta rawaito cewa an kai wadanda suka jikkata zuwa asibitin Messassi dake kusa.

Asibitin ya cika makil inda aka ce ba zai iya kula da duk wadanda suka jikkata ba, kuma an sa wasu asibitoci hudu su taimaka, kamar yadda TheCable ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An samu rahoton mutuwar mutane takwas, mata biyu ‘yan shekara talatin, maza hudu su ma 'yan shekaru talatin, yaro daya, wata gawa daya da danginta suka tafi da ita, in ji wani rahoton kamfanin dillancin labarai na AFP.

An kuma bayar da rahoton tattake wani jariri da jama’a suka yi yayin turmutsitsi a filin wasan na kwallon kafa, inji kafar yanar gida ta Linda Ikeji.

Shugaban jamhuriyar Kamaru Paul Biya ya ba da umarnin gudanar da bincike kan lamarin, ya kuma kara da cewa za a iya samun karin asarar rayuka idan ba a kula ba, yana mai cewa:

Kara karanta wannan

Dare daya: Shekaru 18 basu kwana a kan gado ba saboda talauci, an canza rayuwarsu

"Ba mu da ikon ba ku jimillar adadin wadanda suka mutu."

Kocin Tunusiya, kyaftin da yan wasa 11 sun kamu da Korona, ba zasu buga wasa da Najeriya ba

A wani labarin, yayin da ake shirin buga wasar kifa daya kwala na gasar kofin nahiyar Afrika (AFCON) tsakanin Najeriya da Tunisiya ranar Lahadi, da alamun yan adawan Najeriya sun samun babban matsala.

Kocin yan kwallon Tunisiya, Mondher Kebaier, da yan wasansa goma sha biyu (12) sun kamu da cutar Korona.

An nemi kocin an rasa lokacin hira da manema labarai ranar Asabar a filin kwallon Roumdje Adjia, Garoua.

Asali: Legit.ng

Online view pixel