Dare daya: Shekaru 18 basu kwana a kan gado ba saboda talauci, an canza rayuwarsu

Dare daya: Shekaru 18 basu kwana a kan gado ba saboda talauci, an canza rayuwarsu

  • Wasu ma'aurata a Murang'a sun samu dalilin farin ciki bayan masu yi musu fatan alheri sun ba su kyautar gida na dindindin
  • Karkashin jagorancin mawakiya Anne Lawrence an ce ma'auratan na rayuwa ne a cikin mawuyacin hali kuma ba su samu gatan kwanciya a kan gado ba tsawon shekaru
  • Iyalin sun fada cikin bakin talauci bayan da mai gidan ya samu nakasar shanyewar barin jiki saboda cutar tarin fuka da ya yi fama dashi

Wasu ma'aurata a garin Kandara da ke Murang'a na kasar Kenya na cikin farin ciki bayan da masu hannu da shuni suka kawo musu dauki bayan shafe shekaru suna rayuwa cikin kunci tare da 'ya'yansu.

Peter Waweru, wanda ya kwashe shekaru da yawa baya iya motsawa bayan fama da rashin lafiya, yana zaune ne tare da iyalansa a wani gidan da ke daf da rugujewa.

Kara karanta wannan

Zamfara: Matawalle ya ce suna shirin tona asirin masu aiki tare da ƴan ta'adda

Gidan da aka gina wa talakawa
Shekaru 18 basu kwana a kan gado ba saboda talauci, yanzu rayuwarsu ta canza | Hoto: Anne Lawrence
Asali: Facebook

An yi sa'a, wasu mutanen kirki karkashin jagorancin mawakiyar Kikuyu, Anne Lawrence, sun tausaya musu ganin irin mawuyacin halin da suke ciki, inda suka fara fafutukar ginawa Waweru da iyalinsa gida mai mai har ma da bandakinsa.

Fafutukar da aka fara a karshen 2021 ya kare ne a watan Janairu, abokai da dangi sun hallara a gidan ma'auratan don bikin bude gidan mai dakuna masu yawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Cutar da ke damun Waweru

Yayin da take ba da labarinsu ga mahalarta taron, Anne Lawrence ta ce matar mutumin, Margaret ta zauna tare da mijinta har ta kai ga zama mai ciyar da iyalin bayan fadawar mijinta rashin lafiya.

A cewarta:

“Wannan mutumin ya yi fama da rashin lafiya shekaru bakwai da suka wuce, kuma matarsa tana zaune tare da shi, jama’ar wannan unguwar sun yi mata ba’a sosai.”

Kara karanta wannan

Tsagwaron barna: Wasu miyagun 'yan bindiga sun fille kan tsoho mai shekaru 65

Waweru ya kamu da cutar tarin fuka har ta kai ga ya zama gurgu, matarsa, saboda haka, ta zama mai daukar nauyin gidan.

Anne ta kara da cewa:

"Ya ce mani jarumarsa a rayuwa zata kasance matarsa har abada kuma idan har zai taba yin maganar wani babban mutum, wannan mutumin zai zama matarsa ce."

A kasa suke kwana tsawon shekaru

Iyalin sun sami kyautar gida mai kyau tare da kayan daki haka kuma a cewar mawakiyar, Waweru da matarsa ba su kwana a kan gado ba sama da shekaru 18.

A cewarta:

"A matsayinsu na ma'aurata, suna kwana a kasa, sun yi aure shekaru 22."

A nasu bangaren, ma’auratan sun yi godiya ga masu hannu da shuni da suka kawo musu dauki domin suna bukatar taimako.

A shafinta na Facebook, Anne ta kasa boye farin cikinta bayan kammala aikin.

Ta rubuta a Facebook cewa:

“Fiye da shekara 18 ba su kwana a kan gado a aurensu, daren nan kamar hutun amarci ne a wurinsu. Mun gode wa Jehobah da ya yi amfani da mu."

Kara karanta wannan

Matashi da kanwarsa sun bayyana yadda tsawo da girman jikinsu ya zamo musu matsala

A wani labarin, ‘yan Najeriya sun yi wa wani dan talla fatan alheri bayan da bidiyonsa da yake nuna kirkinsa ga fursunonin da ke cikin motar gidan gyaran hali ya yi ta yawo a shafukan sada zumunta.

A cikin wani faifan bidiyon da aka yada a shafin Instagram, dan Najeriyan da ke sana’ar tallan ruwan sha ya tunkari wata motar gidan gyaran hali da ke dauke da fursunoni.

Da kayansa na ruwan kwalba a kansa, dan tallan ya mika wa fursunoni makudan kudade ta taga. Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a yayin da ake cinkoson ababen hawa a unguwar Ajah da ke Legas.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel