Yanzu-yanzu: Kocin Tunusiya, kyaftin da yan wasa 11 sun kamu da Korona, ba zasu buga wasa da Najeriya ba

Yanzu-yanzu: Kocin Tunusiya, kyaftin da yan wasa 11 sun kamu da Korona, ba zasu buga wasa da Najeriya ba

  • Kasar Tunisiya ta samu babban mushkila yayinda take shirin karawa da Najeriya a wasar zagaye na biyu
  • Najeriya ta haye zagaye na biyu bayan lashe wasanninta uku, yayinda Tunisiya ta haye cikin sa'a
  • Ranar Lahadi za'a buga wasan kifa daya kwala a filin wasan Roumdje Adjia a Garouwa

Garoua - Yayinda ake shirin buga wasar kifa daya kwala na gasar kofin nahiyar Afrika (AFCON) tsakanin Najeriya da Tunisiya ranar Lahadi, da alamun yan adawan Najeriya sun samun babban matsala.

Kocin yan kwallon Tunisiya, Mondher Kebaier, da yan wasansa goma sha biyu (12) sun kamu da cutar Korona.

An nemi kocin an rasa lokacin hira da manema labarai ranar Asabar a filin kwallon Roumdje Adjia, Garoua.

Mataimakinsa, Jalal Al-Qadri, ne yayi hira da manema labarai, rahoton TheCable.

Kara karanta wannan

Bayan an yi waje da zakarun 2019, Super Eagles sun san da wa za su hadu a AFCON

Ya ce Kyaftin dinsu, Wahbi Khazri, da wasu yan wasa koma sha daya (11) sun kamu da cutar Korona kuma ba zasu samu damar musharaka a wasarsu da Najeriya ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kocin Tunusiya, kyaftin da yan wasa 11 sun kamu da Korona
Yanzu-yanzu: Kocin Tunusiya, kyaftin da yan wasa 11 sun kamu da Korona, ba zasu buga wasa da Najeriya ba
Asali: Instagram

Sauran yan wasan sune Aissa Laidouni, Dylan Bronn, Ghaylène Chaalali, Ellyes Skhiri, Anis Ben Slimane, Mohamed Romdhane, Ali Maâloul, Ben Hmida, Aymen Dahmen Yoann Touzgha da Issam Jebali.

Bayan haka kuma, an dakatad da mai tsaron gidansu, Farouk Ben Mustapha.

Asali: Legit.ng

Online view pixel