Tattalin arziki: Kasashen Afrika 5 kanana da za su fi Najeriya habakar tattalin arziki a 2022

Tattalin arziki: Kasashen Afrika 5 kanana da za su fi Najeriya habakar tattalin arziki a 2022

  • Gwamnatin tarayya ta yi hasashen cewa tattalin arzikin kasar nan zai habaka da 4.2% cikin 100% a kasafin kudin da ta sanya wa hannu na 2022 kwanan nan
  • Sai dai kuma IMF ta yi imanin cewa a hakikani kasar za ta bunkasa da 2.7% kasa da matsakaicin 3.8% na kasashen Afrika duk da girman tattalin arzikin Najeriya
  • IMF ta kuma kara bayyana Ghana da wasu kasashen Afirka hudu a matsayin kasashe masu karfin tattalin arziki fiye da Najeriya

Tattalin arzikin Najeriya zai bunkasa a cewar Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) amma ba kamar yadda ake so ba daga kasashen Afirka a 2022.

Kasashen da za su taka rawa a fannin tattalin arziki sun hada da Rwanda, Jamhuriyar Benin, Seychelles, Ghana da Senegal, duk an yi hasashen za su samu ci gaban tattalin arziki a 2022.

Kara karanta wannan

'Yan crypto sun shiga tasku: Miliniyoyi a duniyar crypto sun karye, harka ta kara lalacewa

A cewar IMF, tattalin arzikin kasashen biyar zai bunkasa cikin sauri fiye da matsakaicin habakar kasashen Afirka na yankin sahara da 3.8% a 2022.

Tattalin arzikin Najeriya ka iya karuwa
Tattali: Kasashen Afrika kanana da za su fi Najeriya habakar tattalin arziki a 2022 | Hoto: nairametrics.com
Asali: Getty Images

IMF ta ce Rwanda za ta karu da 7% cikin 100% a 2022 yayin da tattalin arzikin Jamhuriyar Benin zai karu da 6.5%.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Seychelles kasar da yawon bude ido ke habaka tattalin arzikinta zata shaida karuwar 8% yayin da mutane da yawa ke yin allurar rigakafin korona a duniya kuma suke kokarin tafiya yawace-yawacen bude ido.

Tattalin arzikin Ghana da Senegal kuma za su habaka da 6.2% da kashi 5.5% a cikin watanni 12 na 2022.

Hasashen bunkasar tattalin arzikin Najeriya a 2022

Tattalin arzikin Najeriya a cewar IMF ana sa ran zai bunkasa da 2.7% kari kadan daga 2.6% da kasar ta yi hasashe a 2021.

Kara karanta wannan

Idan kuka kara farashin mai, zaku sake jefa miliyoyin mutane talauci: Janar AbdulSalam

Cibiyar ta IMF da ke Washington ta ba da misali da farfadowar da aka samu a sassan da ba na mai ba da kuma hauhawar farashin danyen mai a matsayin abubuwan da ke haifar da wannan ci gaba.

Gwamnatin Najeriya ta yi tsammanin habakar tattalin arziki

A bangare guda, Vanguard ta ruwaito cewa karuwar 2.7% da IMF ta yi kiyasi kan Najeriya a 2022 ya nuna ragin 1.5%, kasa da 4.2% na hangen da gwamnatin tarayya ta yi hasashenta na 2022 a cikin daftarin kasafin kudinta na 2022 zuwa 2024.

Ministar kudi ta Najeriya, Misis Zainab Ahmed ta yi sharhi kan Tsarin 2022 zuwa 2024 MTFF/FSP ta ce:

“A 2022, muna sa ran za a samu karin 4.2%, sannan a samu raguwar 2.3% a 2023 da kuma karin 3.3% a 2024.”

A wani labarin, Bitcoin da sauran manyan kudaden intanet sun yi faduwar kusan Naira tiriliyan 54 a cikin sa'o'i 24 yayin da suke ci gaba da faduwar kasa, faduwar da ta fara sama da makonni biyar a jere kenan.

Kara karanta wannan

Watan Yuni zamu yanke shawara kan kara farashin litan man fetur, Majalisar tattalin arzikin Najeriya

Bitcoin ya ragu da kusan 4% cikin 100% akan Naira miliyan 14, in ji Coin Metrics da Ether mai faduwar kusan 7% bisa 100% zuwa Naira miliyan biyu.

A ranar Litinin, 24 ga Janairu, 2022, dukansu sun yi kasa a matsayi mafi karanci tun watan Yulin bara. Haka kuma sun fadi da 50% cikin 100% na kololuwar darajarsu a tarihin crypto, a cewar wani rahoton CNBC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel