Idan kuka kara farashin mai, zaku sake jefa miliyoyin mutane talauci: Janar AbdulSalam

Idan kuka kara farashin mai, zaku sake jefa miliyoyin mutane talauci: Janar AbdulSalam

  • Majalisar tattalin arzikin tarayya ta bayyana lokacin da gwamnati za ta yanke shawarar kara farashin man fetur
  • Tsohon Shugaban kasan Najeriya yace idan gwamnati ta kara farashin miliyoyin yan Najeriya zasu talauce
  • NEC ta baiwa gwamnatin tarayya shawarar a kara farashin litan man fetur zuwa N302 nan da watan Febrairu

Abuja - Tsohon Shugaban kasan mulkin Soja, Janar AbdulSalami Abubakar, ya yi gargadi game da shirin kara farashin litan man fetur da gwamnatin tarayya ke shirin yi.

A jawabin da ya gabatar ranar Alhamis a taron tattaunawa kan halin da kasa ke ciki da Daily Trust ta shirya a Abuja, tsohon Sojan yace hakan na da hadari.

A cewarsa, sama da yan Najeriya milyan 18 yanzu haka na fama da bakar talauci da bai kamata ba kuma annobar COVID-19 ta sake tsananta lamarin.

Kara karanta wannan

Watan Yuni zamu yanke shawara kan kara farashin litan man fetur, Majalisar tattalin arzikin Najeriya

Yace:

"Matsalar tsaro ta lalata tattalin arzikinmu. Rashin aikin yi da kuma rashin samun isasshen kudi ga masu aiki ya yi muni. Sama da yan Najeriya milyan 18 na cikin talauci mara amfani."
"Farashin kayan abinci na cigaba da hauhawa kuma yan Najeriya sun fara gaza siya. Duk da haka, ana shirin kara farashin man fetur kamar yadda aka sanar a Nuwamba. Dukkanmu mun san idan haka ya faru, za'a jefa miliyoyin yan Najeriya cikin talauci."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Idan kuka kara farashin mai, zaku sake jefa miliyoyin mutane talauci: Janar AbdulSalam
Idan kuka kara farashin mai, zaku sake jefa miliyoyin mutane talauci: Janar AbdulSalam
Asali: UGC

A kara farashin litan mai zuwa N302 nan da Febrairu, kwamitin El-Rufa'i ta bada shawara

A jiya kun ji cewa Majalisar NEC ta baiwa gwamnatin tarayya shawarar a kara farashin litan man fetur zuwa N302 nan da watan Febrairu 2022.

Wannan shawara na cikin jeringiyar shawarin da kwamitin NEC mai tattaunawa da kamfanin mai NNPC kan farashin man da ya kamata a sanya a Najeriya ta bada, rahoton TheCable.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Najeriya ba ta buƙatar shugaban ƙasa na ƙabilanci, Hakeem Baba-Ahmed

Wannan kwamiti dake karkashin jagorancin gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ta gabatar da shawarin.

A 2021, NEC karkashin mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ta nada kwamitin sakamakon rashin kudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel