'Yan crypto sun shiga tasku: Miliniyoyi a duniyar crypto sun karye, harka ta kara lalacewa

'Yan crypto sun shiga tasku: Miliniyoyi a duniyar crypto sun karye, harka ta kara lalacewa

  • 'Yan crypto za su tuna da sa'o'i 24 da suka gabata a rayuwarsu cikin hawaye yayin da lalitansu suka zama fanko biyo bayan faduwar darajar Bitcoin
  • A ranar Juma'a, 21 ga Janairu, tsabar Bitcoin ta nutse kasa kusan $38,000, dungurawar kusan 7% na ainihin farashinta
  • An yi gargadi da yawa cewa 'yan crypto za su tafka asarar biliyoyi na Bitcoin a cikin shekaru masu zuwa nan kusa

Masu zuba kudadensu a duniyar crypto sun fuskanci babbar asara a sashen Bitcoin da wasu tsabobin crypto suka rage darajar ta shafe sama da N296.68bn na kadarori a cikin kasa da sa'o'i 24.

Bayanai daga CoinDesk sun nuna cewa Bitcoin ya fadi da kasa da 8% kuma koma kan farashin $38,5K a farkon sa'o'in ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Damfarar N299.86m: Kotu na neman wani tsohon dan takarar gwamnan Zamfara

Bitcoin ta saka 'yan crypto hawaye
'Yan crypto sun shiga tasku: Miliniyoyi a duniyar crypto sun karye, harka ta kara lalacewa | Hoto: nairametrics.com
Asali: Getty Images

Faduwar darajar Bitcoin ta kai ga durkusar da lalitun 'yan crypto sama da 185,480 inda akalla suke bukatar neman sabon jari don ci gaba da harkalla.

Kwararru sun yi gargadi a baya cewa Bitcoin na iya faduwa kasa da $40K saboda damuwar da ake fuskanta na hauhawar farashin da kuma shawarar hana crypto da a kasar Rasha, in ji Nairametrics.

Karshe ma, tun watan Nuwamba, farashin Bitcoin ya ragu da fiye da 40% daga kolouwar farashin da ya taba kaiwa na $69K, inda har yanzu kasuwar ke ci gaba da kara lalacewa.

Sauran asarar da aka tafka

Ethereum, na biyu a daraja a duniyar crypto, ya nutse da 8% a cikin sa'o'i 24 da suka gabata. Farashinsa ya kowa kasa zuwa $2,860, ini bayanan da aka gani daga kafar musaya ta FTX.

Kara karanta wannan

'Kazamin sasanci: An kama su da satar ɗanyen man fetur na Naira miliyan 200, za su biya N2,000 kacal a sake su, Alƙalin kotu ya koka

Mafi girman oda guda na daya ya faru akan kafar Bitmex kenan - XBTUSD kusan darajar $9.91 miliyan.

Binance yana da mafi yawan madarar kudi a duk kafafen musayar cryto, akalla akwai $173m, kusan 91% daga cikin kudaden sun kasance jarin dogon zango.

A matsayi na biyu shine kafar musaya ta Okex wanda ya fi karbuwa a yankin Asiya, yana da jarin akalla $170m na dogon zango.

A watan Disamban 2021, 'yan crypto sun tafka babban faduwa a ranar Asabar bayan Bitcoin da wasu tsabobin intanet suka rage darajar sama da dala biliyan daya.

Wannan na faruwa ne yayin da 'yan crypto a duniya suka sayar da tsabobin kudaden intanet don daidaituwa da amintattun hannayen jari yayin da bukukuwan Kirsimeti ke gabatowa.

Bitcoin shine mafi daraja a tsabobin kudaden intanet a daraja ta kasuwa, ya fado da 31.6% daga darajar $69,000 mafi girma a shekarar nan a ranar 10 ga Nuwamba.

Kara karanta wannan

Babbar magan: Gwamna ya sanya hannu ya doka mai tsauri ta hana kiwo a fili

Asali: Legit.ng

Online view pixel