Rikici: Sojoji sun kwamushe shugaban Burkina Faso suna shirin kifar da gwamnatinsa

Rikici: Sojoji sun kwamushe shugaban Burkina Faso suna shirin kifar da gwamnatinsa

  • Rahotanni sun tabbatar da cewa Burkina Faso na cikin fargaba cewa wasu sojojin da sun yi wa shugaban kasar kawanya
  • Majiyoyi sun ce an kama shugaba Roch Kabore na kasar kuma jami'an soji dauke da makamai suna tsare da shi a halin yanzu
  • Sojojin na neman gwamnatin Burkina Faso da ta samar da karin kudade da za su taimaka wa sojoji wajen yakar masu tada kayar baya

Burkina Faso - A ranar Lahadi 23 ga watan Junairu ne sojoji suka tsare shugaban kasar Burkina Faso Roch Kabore, kamar yadda wasu majiyoyin kasa da kasa suka bayyana.

Sojojin da ke dauke da makamai sun kuma yiwa hedikwatar gidan talabijin din kasar kawanya a yayin da ake ta harbe-harbe a kusa da fadar shugaban kasa da barikin soji da ke Ouagadougou babban birnin kasar.

Kara karanta wannan

2023: Miyetti Allah ta ce ta na bayan Tinubu, ta bayyana taimakon da ya yi mata a baya

Shugaban Burkina Faso na iya fuskantar fushin soji
Rikici: Sojoji sun kwamushe shugaban Burkina Faso a shirin kifar da gwamnatinsa | Hoto: news24.com
Asali: UGC

BBC ta rawaito cewa sojojin na bukatar a kori hafsan sojin Burkina Faso sannan a samar da karin kudade ga sojoji a yakin da ake yi da ta'addanci.

Sai dai Bathelemy Simpore, ministar tsaron kasar ta musanta cewa an yi juyin mulki a kasar kuma an kama shugaba Kabore, in ji rahoton Al Jazeera.

A cewar Simpore a gidan talabijin na kasar:

“Ba a tsare shugaban kasa ba; Babu wata cibiya ta kasar da aka yi wa barazana.
“A yanzu, ba mu san manufarsu ko abin da suke nema ba. Muna kokarin tuntubar su."

A halin da ake ciki, gwamnatin kasar ta sanya dokar hana fita daga karfe 8 na dare zuwa 5:30 na safe har sai an samu sauki, yayin da aka ba da umarnin rufe makarantu a fadin kasar na tsawon kwanaki biyu.

Kara karanta wannan

Sabon harin ta'addanci: 'Yan bindiga sun afkawa sansanin sojoji a Katsina, sun yi barna

An damke Sojoji 40 da sukayi kokarin juyin mulki a kasar Sudan

A wani labarin, wasu jami'an Sojoji sun yi yunkurin juyin mulki ranar Talata kuma an damke yawancin Sojojin, a cewar wasu manyan jami'an gwamnatin kasar da Sojoji ga tashar CNN.

An damke kimanin Sojoji 40 da sukayi kokarin kwace gidan talabijin da hedkwatar Sojojin kasar, wani babban jami'in kasar da aka sakaye sunansa ya fada.

Bayan rashin nasarar da aka yi na juyin mulki, an baza jami'an tsaro cikin birnin Khartoum.

Asali: Legit.ng

Online view pixel