An damke Sojoji 40 da sukayi kokarin juyin mulki a kasar Sudan
- An damke wasu daga cikin wadanda sukayi kokarin juyin mulki a Sudan
- An baza Sojoji cikin gari don tabbatar da tsaro
- Wannan na zuwa shekaru biyu bayan yiwa shugaba Albashir juyin mulki
Wasu jami'an Sojoji sun yi yunkurin juyin mulki ranar Talata kuma an damke yawancin Sojojin, a cewar wasu manyan jami'an gwamnatin kasar da Sojoji ga tashar CNN.
An damke kimanin Sojoji 40 da sukayi kokarin kwace gidan talabijin da hedkwatar Sojojin kasar, wani babban jami'in kasar da aka sakaye sunansa ya fada.
Bayan rashin nasarar da aka yi na juyin mulki, an baza jami'an tsaro cikin birnin Khartoum.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An yi yunkurin juyin mulki a Sudan
Gidan talabijin ta kasar Sudan ta tabbatar da yunkurin juyin mulki a kasar.
Har yanzu dai ba'a san ainihin wadanda suka shirya juyin mulkin ba.
Jaridar Reuters ta ruwaito kakakin gwamnati Mohamed Al Faki, da cewa ba da jimawa ba za a fara binciken wadanda ake zargi da kitsa juyin mulkin.
Wannan na zuwa ne shekaru biyu bayan kifar da gwamnatin tsohon Shugaba Omar Albashir, sannan a ka kafa gwamnatin riko da ta kunshi sojoji da fararen hula.
An samar da gwamnatin hadaka ta sojoji da wakilan fararen hula da kungiyoyin masu zanga-zanga bisa yarjejeniyar kara-karba bayan kifar da Shugaba Bashir a shekarar 2019.
Asali: Legit.ng