Labari mai dadi: Farashin mai ya cilla $88 a kowace ganga, karo na farko tun hawan Buhari

Labari mai dadi: Farashin mai ya cilla $88 a kowace ganga, karo na farko tun hawan Buhari

  • Farashin danyen mai ya yi tashin gwauron zabi a kasuwannin duniya, karo na farko tun 2014 kafin Buhari ya hau mulki
  • Rahoton da muka samo daga majiyoyi ya bayyana yadda kungiyar OPEC+ ta taka rawa wajen daga farashin a shekarar nan
  • Kasashe da dama an bayyana sauyin farashin da suka samu, inda na Najeriya ya haura sama da $88 kan kowace ganga

Jaridar TheCable ta rahoto cewa, farashin danyen mai na Brent, ya tashi zuwa $88 a kowacce ganga a ranar Talata, bisa tsauraran matakan da kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta OPEC da kawayenta ke samarwa.

A ranar Talata, makomar danyen mai na Brent ya samu 1.65% zuwa $88.11 kan kowace ganga daya a karfe 8:41 GMT+1, yayin da US West Texas Intermediate ya karu da 20.8% zuwa $85.73, 0.54% na ICE na London da ya kai $87, in ji rahoton APA.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kama mutumin da ake zargi da kwantawa da yar shekara 80 a Nasarawa

Farashin man fetur ya tashi a duniya
Labari mai dadi: Farashin mai ya cilla $88 a kowace ganga, karo na farko tun hawan Buhari | Hoto: lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Morgan Stanley, wani bankin zuba jari na kasa da kasa, ya yi hasashen cewa danyen mai na Brent zai iya haura $90 a cikin kwata na uku na wannan shekarar.

Makonni biyu da suka gabata, OPEC+ ta yanke shawarar ci gaba da shirin kara ganga 400,000 na mai a kowace rana a watan Fabrairu - wanda ya haifar da hauhawar farashin mai da kuma habaka a kasuwannin mai na duniya.

Louise Dickson, wata babbar manazarciya kan kasuwannin mai na Rystad Energy, ta lura cewa karfin kasuwar da ke bayan karuwar farashin zai ci gaba da tsananta a shekarar 2022.

Bloomberg ta nakalto Dickson na cewa:

"Kyakkyawan yanayin farashin ya shiga cikin mako na uku na Janairu, kuma abubuwan da ke bayan kyakkyawan yanayin suna ci gaba da karfafa hakan har zuwa 2022."

Kara karanta wannan

Matashi da kanwarsa sun bayyana yadda tsawo da girman jikinsu ya zamo musu matsala

Farashin man fetur ya samu karuwar sama da 10% cikin 100% a 2022 - wani bangare kenan saboda karancin shigar da kaya daga mambobin kungiyar OPEC+, ciki har da Najeriya da Libya.

A cikin watan Disamba, kamfanin Shell Petroleum Development Company of Nigeria (SPDC) ya ba da sanarwar hana fitar da danyen mai na Forcados na Najeriya zuwa kasashen waje, bayan da wani jirgin ruwa ya samu cikas a hanyar da tankokin mai suke bi.

Farashin yanzu ya haura $62 akan kowacce ganga da aka ware a kasafin kudin 2022.

NNPC na kokarin ragargaza farashin gas, ta bayyana matakin da ta ke dauka

A wani labarin, Malam Mele Kyari, manajan daraktan matatar man fetur ta kasa (NNPC), ya alakanta tashin farashin gas din girki da yadda farashin danyen man fetur ya tashi a kasuwannin duniya.

Jaridar Guardian ta ruwaito cewa, Kyari ya sanar da hakan ne yayin kaddamar da ma'adanar kamfanin Emadeb Energy Services Limited mai daukar 120MT na LPG a Abuja.

Kara karanta wannan

Tiwa Savage: Na so ace Dangote mahaifi na ne, amma kash

Sai dai ya tabbatar wa da 'yan Najeriya cewa, matatar na yin duk kokarin da ya dace wurin tabbatar da ta kara yawan LPG da ake samarwa domin ragargaza farashinsa, Guardian ta ruwaito hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel