Labari mai dadi: NNPC na kokarin ragargaza farashin gas, ta bayyana matakin da ta ke dauka

Labari mai dadi: NNPC na kokarin ragargaza farashin gas, ta bayyana matakin da ta ke dauka

  • Manajan daraktan matatar man fetur ta kasa, NNPC, Malam Mele Kyari, ya ce matatar man fetur ta kasa na kokarin ragargaza farashin iskar gas
  • Kamar yadda Kyari ya bayyana, farashin ya yi sama ne saboda karancinsa wanda za a fara samar da shi da yawa domin saukar da kudinsa warwas
  • Kyari ya sanar da cewa, tashin gwauron zabi da farashin danyen man fetur da sauran kayayyakin suka yi ya taka rawar gani wurin tayar da fashin

Abuja - Malam Mele Kyari, manajan daraktan matatar man fetur ta kasa (NNPC), ya alakanta tashin farashin gas din girki da yadda farashin danyen man fetur ya tashi a kasuwannin duniya.

Jaridar Guardian ta ruwaito cewa, Kyari ya sanar da hakan ne yayin kaddamar da ma'adanar kamfanin Emadeb Energy Services Limited mai daukar 120MT na LPG a Abuja.

Kara karanta wannan

Rikicin APC a Zamfara: Tsohon kwamishina ya bar tsagin Yari ya koma na Matawalle

Labari mai dadi: NNPC na kokarin ragargaza farashin gas, ta bayyana matakin da ta ke dauka
Labari mai dadi: NNPC na kokarin ragargaza farashin gas, ta bayyana matakin da ta ke dauka. Hoto daga guardian.ng
Asali: UGC

Sai dai ya tabbatar wa da 'yan Najeriya cewa, matatar na yin duk kokarin da ya dace wurin tabbatar da ta kara yawan LPG da ake samarwa domin ragargaza farashinsa, Guardian ta ruwaito hakan.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa, mazaunan Abuja da yankunan suna siyan 12kg na gas din girki kan farashin N8,500 da N9,500 a maimakon tsohon farashin N4,000 da N6,000.

Kamar yadda Mele Kyari yace:

"Abubuwa biyu ne suka sanya hakan, daya daga ciki shi ne yawan da ake samarwa yayin da dayan kuma ya zama farashinsa na duniya. Shi kuma farashi ya na tafiya ne da kowanne kayan man fetur har da danyensa. Don haka wannan yana nuna halin da kasuwar duniya ta ke ciki.
"Abinda mu ke yi yanzu shi ne kara yawan shi. Matukar aka kara yawan gas da ake samarwa, dole farashin zai sauka."

Kara karanta wannan

Bayan shekaru 2 ana wahala, Bill Gates ya fara hango karshen annobar annobar COVID-19

Ba mu da hurumin daidaita farashin gas din girki, Gwamnatin tarayya

A wani labari na daban, gwamnatin tarayya a ranar Talata ta ce ba ta da hurumin daidaita farashin iskar gas ta girki saboda abu ne wanda kasashen duniya ke daidaitawa.

Karamin ministan man fetur, Timipre Sylva, wanda ya sanar da hakan ga manema labarai na gidan gwamnati, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fada damuwa sakamakon tashin farashin gas din girkin, Tribune Online ta ruwaito.

Ministan man fetur din ya je fadar shugaban kasa da ke Abuja inda ya gabatar masa da Injiniya Faruk Ahmed, shugaban NMDPRA da Injiniya Gbenga Komolafe shugaban NUPRC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel