Tiwa Savage: Na so ace Dangote mahaifi na ne, amma kash

Tiwa Savage: Na so ace Dangote mahaifi na ne, amma kash

  • Shahararriyar mawakiya, Tiwa Savage ta yi korafi kan wahalar da ke tattare da neman kudi da kasancewa dan talaka
  • Tiwa ta kuma bayyana cewa ta so ace mai kudin Afrika, Aliko Dangote ne mahaifinta
  • Sai dai duk da haka ta nuna alhini da jimamin rashin mahaifinta, inda tace tayi kewar shi sosai

Shahararriyar mawakiyar nan ta Najeriya, Tiwa Savage, ta bayyana cewa ta so ace mai kudin Afrika, Aliko Dangote, ne mahaifinta, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Savage ta je shafinta na zumunta a ranar Alhamis, 13 ga watan Janairu, don yin korafin wahalar da ke tattare da neman kudi.

Tiwa Savage: Na so ace Dangote mahaifi na ne, amma kash
Tiwa Savage: Na so ace Dangote mahaifi na ne, amma kash Hoto: @tiwasavage, @dangote_fanpage
Asali: Instagram

Ta rubuta:

"Ina da ganawa guda daya nan gaba. Neman kudi ba abu mai sauki bane fa. Allah ka taimake ni, amma me yasa babana ba Dangote bane ko wani abu makamancin haka (Allah ya ji kansa)."

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Na shirya yin gaba da gaba da Tinubu a zaben fidda gwanin APC – Shahararren sanata

Kalli wallafar a kasa:

Mahaifin mawakiyar ya mutu a ranar 19 ga watan Janairu, 2021, an kuma binne shi a Lagas jim kadan bayan ta saki wakarta ‘Water and Garri’.

A yayin da take sanar da rasuwar mahaifinta a dandalin sada zumunta, mawakiyar ta bayyana shi a matsayin jajirtaccen mutum.

"Ka yi fafutaka har zuwa karshe, ka sha gwagwarmaya baba, ka sha fama tsawon shekarun nan da suka gabata amma kana hutawa a yanzu. Bai zo mani da sauki ba, ba ni da karfi, na yi rauni sosai. Ka huta lafiya sarakina. Ina kaunarka, baba."

Na yi murabus daga ɗirka wa 'yan mata ciki, Mawaƙi 2Baba

A gefe guda, shaharraen mawakin Najeriya da ya lashe kyaututuka da dama, Innocent Idibia da aka fi sani da 2Baba ya bayyana cewa ba zai sake yi wa wata mace ciki ba, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shehu Sani: 'Yan bindiga sun zama jiha mai zaman kanta a cikin jihohin Arewa maso Yamma

Mawakin, da ya yi wakar 'African Queen' ya bayyana hakan ne cikin wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta yayin bikin al'adu da kadade ta Idoma International Carnivial da aka yi a Otukpo, garinsu su 2Baba a Jihar Benue.

A cikin faifan bidiyon, Shugaban kamfanin Hypertek Digital ya yi magana ne cikin harshen Pidgin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel