Dr Hamid Choi: Dan Koriya na farko da ya fassara Qur'ani da Sahihul Bukhari da yaren kasar

Dr Hamid Choi: Dan Koriya na farko da ya fassara Qur'ani da Sahihul Bukhari da yaren kasar

  • Dr Hamid Choi Yong Kil ne Musulmi na farko dan asalin kasar Koriya ta Kudu da ya fassara Qur'ani da Sahihul Bukhari zuwa yarensu
  • Mai da'awar kuma lakcaran, ya kwashe shekaru kusan bakwai ya na wannan aikin kafin ya kammala shi gaba daya
  • Malamin masoyi ne ga Samahatusy Shaykh Abdul Aziz bin Baz, tsohon shugaban jami'ar Musulunci ta Madina
  • Hazakarsa, kamun kansa da mutuncinsa ne yasa shugaban makarantarsu a wannan lokacin ya ke kaunarsa don har gayyatarsa ya ke gidansa

Koriya ta Kudu - A tarihin duniya baki daya, ba a taba fassara Qur'ani da Sahih Bukhari ba zuwa harshen Koriya sai yanzu. Dr Hamid Choi Yong Kil ne mutum na farko kuma Musulmin kasar Koriya da yayi aikin, The Islamic Information ta ruwaito.

Ya kwashe kusan shekaru bakwai kafin ya kammala wannan fassarar. Malami ne mai da'awa kuma lakcara ne a fannin ilimin addinin Musulunci da Larabci a jami'ar Koriya ta kudu.

Kara karanta wannan

Allah ya yiwa tsohon Shugaban Majalisar koli ta Shari'a, Dr Datti Ahmad, rasuwa

Dr Hamid Choi: Dan Koriya na farko da ya fassara Qur'ani da Sahihul Bukhari da yaren kasar
Dr Hamid Choi: Dan Koriya na farko da ya fassara Qur'ani da Sahihul Bukhari da yaren kasar. Hoto daga theislamicinformation.com
Asali: UGC

A lokacin da ya kammala karatunsa a jami'ar Musulunci da ke Madinah, Samahatusy Shaykh Abdul Aziz bin Baz, shi ne shugaban makarantar. A nan ya samu iliminsa mai tarin yawa. Babu shakka shehin Malamin ya na da wuri na musamman a zuciyar Choi.

Sau da yawa, shehin malamin kan gayyacesa zuwa gidansa inda ya ke karrama shi. Asalin kasar kuwa kasa ce da ke da karancin Musulmi, The Islamic Information ta ruwaito.

Tarin ilimin sa tare da kamewarsa da kuma mutuncinsa ne ke birge Shaikh bin Baz sosai.

Qur'ani da sahihul Bukhari da ya fassara suna daga cikin tarin ayyukan kimiyyarsa. Ya rubuta sama da littafai 90 da kansa inda wasu ya fassara su yayin da wasu ya rubuta da tarin iliminsa.

Kara karanta wannan

Kungiyar MSSN ta fusata da yadda ake kuntatawa masu hijabi a kudu, za ta dauki mataki

Allahu Akbar: Ana gobe Kirsimeti, an mayar da wata gagarumar coci zuwa Masallaci a Turkiyya

A wani labari na daban, wannan al'amarin ya auku ne a Adrianopilis/Edirne a garin Ainos/Enez inda aka mayar da wata katafariyar coci masallaci.

Kamar yadda malaman fannin kashe-kashen Girka suka shaida, kashe-kashen ya fara aukuwa ne a 1913, kafin yakin duniya na daya, Edirne a gabashin Thrace take.

Bayan dawo da cocin bisa umarnin GDI, Cocin Hagia Sophia da ke Ainos (Enez), a Adrianoupolis (Edirne), ta koma masallaci ranar jajibarin Kirsimeti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel