Allahu Akbar: Ana gobe Kirsimeti, an mayar da wata gagarumar coci zuwa Masallaci a Turkiyya

Allahu Akbar: Ana gobe Kirsimeti, an mayar da wata gagarumar coci zuwa Masallaci a Turkiyya

  • Ana gobe ranar Kirsimeti, an mayar da wata katafariyar coci zuwa Masallaci a yankin Adrianopilis/Edirne a garin Ainos/Enez da ke kasar Turkiyya
  • Ali Erbas, shugaban al'amuran addinin Islama na Turkiyya ya bayyana hakan a wallafar da yayi a shafinsa na Twitter
  • Ya sanar da tsananin farin cikin da suke ciki bayan da aka kaddamar da Masallacin inda yayi addu'ar Allah ya cigaba da daukaka Musulunci

Turkiyya - Wannan al'amarin ya auku ne a Adrianopilis/Edirne a garin Ainos/Enez inda aka mayar da wata katafariyar coci masallaci.

Kamar yadda malaman fannin kashe-kashen Girka suka shaida, kashe-kashen ya fara aukuwa ne a 1913, kafin yakin duniya na daya, Edirne a gabashin Thrace take.

Allahu Akbar: Ana gobe Kirsimeti, an mayar da wata gagarumar coci zuwa Masallaci a Turkiyya
Allahu Akbar: Ana gobe Kirsimeti, an mayar da wata gagarumar coci zuwa Masallaci a Turkiyya. Hoto daga theislamicinformation.com
Asali: UGC

Bayan dawo da cocin bisa umarnin GDI, Cocin Hagia Sophia da ke Ainos (Enez), a Adrianoupolis (Edirne), ta koma masallaci ranar jajibarin Kirsimeti.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: An nada Jose Peseiro matsayin sabon Kocin Super Eagles

Masallacin Muhammed mai nasara ya koma masallacin nasara a shekarar 1456 sannan an kara bude shi a matsayin masallacin Muhammed mai Nasara.

Sakamakon girgizar kasar da aka yi a yankin ya sa ba a sake bude cocin ba. Ali Erbas ya kara bude masallacin bayan shekaru 56 don a yi sallar Juma’a.

Rahoton The Echedoros-a.gr ya bayyana yadda Erbas ta dauki Musulunci a matsayin al’ada wacce su ka dauka matukar muhimmanci akan masallaci.

An yi addu’o’i da kuma jawabi bayan yanke kyallen kaddamar da masallacin.

“Bayan an kaddamar da masallacin Hegia Sophia a Istanbul shekarar da ta gabata, ga shi yau mun kara haduwa don kaddamar da masallacin Hegia Sophia a Ainu-Edirne,” kamar yadda shugaban harkokin addini, Ali Erbas ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Kara karanta wannan

Kungiyar MSSN ta fusata da yadda ake kuntatawa masu hijabi a kudu, za ta dauki mataki

Ya kara da cewa:

“Mun kai ziyara Balkans a watannin da suka gabata. Da zarar mun kalli ginin masallacin zuciyarmu tana mana dadi. Ana aiwatar da ibada a masallacin Hagia Sophia a Edirne. Muna fatan Ubangiji ya albarkaci masallacin. Wannan yana nuna hadin kai da soyayya kamar yadda muke a dunkule anan.”

A karon farko, an yi bikin gagarumin bikin Kirsimeti a kasar Saudi Arabiya a 2021

A wani labari na daban, a karon farko, an yi shagulgula na gani da fadi don bikin kirsimeti a kasar Saudiyya. A shekarar 2021 ne mutanen kasar Saudi Arabiya suka sha bukukuwa saboda kirsimeti. Da alamu wannan shekarar an yi shagulgula iri-iri tun bayan dage dokokin kare kai daga cutar korona.

Babu shakka kirsimeti biki ne wanda kiristoci su ke dabbakawa a kowacce karshen shekara kuma ya na kasancewa lokacin rani, Saudi Gazette ta ruwaito.

Kiristoci da dama da ke kasar Saudiyya sun nuna jin dadinsu akan damar da suka samu a karo na farko suka yi shagulgulan kirsimeti a shekarar nan. Duk da dai a shekarun baya su na shagulgulan amma bai bayyana karara ba har ya zama gagarumi kamar na wannan shekarar.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari ya gana da kamfanin Jamus kan yadda za a bullowa aikin jirgin Maradi-Kano

Asali: Legit.ng

Online view pixel