Yanzu-yanzu: An nada Jose Peseiro matsayin sabon Kocin Super Eagles

Yanzu-yanzu: An nada Jose Peseiro matsayin sabon Kocin Super Eagles

  • Bayan makonni da sallamar tsohon kocin Super Eagles, an nada mutumin da aka dade ana hasashe
  • Sabon kocin da aka nada ya taba jagorantar yan kwallon kasashe irinsu Saudiyya da Venezuela a baya
  • Jama'a a kafafen sada zumunta sun tofa albarkatun bakinsu; yayinda wasu suka ce bai taba cin wani kofin kirki ba, wasu sunce a bari a ga kamun ludanyinsa

Hukumar kwallon kafa a Najeriya (NFF) ta alanta nadin Jose Peseiro a matsayin sabon kocin yan kwallon Najeriya Super Eagles.

Wannan sanarwa ta fito ne ranar Laraba a takardar da NFF ta sake., rahoton TheCable.

NFF ta bayyana cewa sabon kocin ba zai fara aiki kai tsaye ba, sai bayan gasar kofin nahiyar Afrika da za'ayi a sabon shekarar 2022 a kasar Kamaru.

Kara karanta wannan

Abubuwa 15 da ya dace a sani a kan tsohon kocin Real Madrid da zai jagoranci S/Eagles

Wani sashen jawabin:

"Bayan dubi cikin rahoton da Shugaban Kwamitin aiki ya gabatar, Kwamitin zartaswa ta amince da nadin Mr Jose Peseiro matsayin sabon kocin Super Eagles, biyo bayan sallamar Gernet Rohr."
"Amma kwamitin ta ce mukaddashin koci, Augustin Eguavoen, ne zai jagorancin Super Eagles a gasar AFCON 2021 da za'ayi a Kamar. Mr Peseiro kawai kallo da lura zai yi."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"An yanke shawarar cewa gasar AFCON wata kafa ce da zata ba Mr Peseiro daman kyautata alakarsa da Mr Eguavoen, kafin ya kama makamar aiki matsayin Jagora bayan AFCON."

Yanzu-yanzu: An nada Jose Peseiro matsayin sabon Kocin Super Eagles
Yanzu-yanzu: An nada Jose Peseiro matsayin sabon Kocin Super Eagles Hoto: www.uefa.com
Asali: UGC

Makonni biyu bayan sallamar Gernot Rohr

Makonni biyu da suka gabata ranar 12 ga Disamba NFF ta tsige kocin kungiyar Super Eagles, Gernot Rohr, ta kuma baiwa Augustine Eguavoen rikon kwarya.

NFF ta sallami Gernot Rohr bayan ya yi shekaru biyar ya na wannan aiki.

Babban sakataren hukumar NFF, Dr. Mohammed Sanusi ya fitar da jawabi ya na cewa tsohon ‘dan wasan Najeriya, Eguavoen, ya sake dawowa kujerar koci.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel