A karon farko, an yi gagarumin bikin Kirsimeti a kasar Saudi Arabiya a 2021

A karon farko, an yi gagarumin bikin Kirsimeti a kasar Saudi Arabiya a 2021

  • A shekarar 2021, Kirsitoci da ke kasar Saudi Arabiya sun yi gagagrumin shagalin bikin Kirsimeti na shekarar nan
  • An dinga jin sautikan wakokin Kirsimeti na tashi daga manyan kantuna yayin da aka kawata su da kalolin ja da fari
  • Mabiya addinin Musulunci ba a bar su a baya ba, sun taya Kiristocin kasar murna inda suka dinga raba kyautukan kayan kwalam

Jeddah - A karon farko, an yi shagulgula na gani da fadi don bikin kirsimeti a kasar Saudiyya. A shekarar 2021 ne mutanen kasar Saudi Arabiya suka sha bukukuwa saboda kirsimeti. Da alamu wannan shekarar an yi shagulgula iri-iri tun bayan dage dokokin kare kai daga cutar korona.

Babu shakka kirsimeti biki ne wanda kiristoci su ke dabbakawa a kowacce karshen shekara kuma ya na kasancewa lokacin rani, Saudi Gazette ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bidiyon Sarkin Bauchi yana rera wakar yabo yayin da ya karbi bakuncin Kiristoci a fadarsa

A karon farko, an yi bikin Kirsimeti a kasar Saudi Arabiya a 2021
A karon farko, an yi bikin Kirsimeti a kasar Saudi Arabiya a 2021. Hoto daga saudigazette.com.sa
Asali: UGC

Kiristoci da dama da ke kasar Saudiyya sun nuna jin dadinsu akan damar da suka samu a karo na farko suka yi shagulgulan kirsimeti a shekarar nan. Duk da dai a shekarun baya su na shagulgulan amma bai bayyana karara ba har ya zama gagarumi kamar na wannan shekarar.

Sakamakon shugabancin Saudiyya yanzu ya zama na shakatawa da walawa, cikin sauki aka yi shagalin kirsimeti inda aka kawata shuguna, wuraren cin abinci da sauransu da ado irin na bikin kirsimeti. Baki suna jin yadda wakokin kirsimeti su ke tashi daga wurare daban-daban.

Mafi yawan kiristocin da ke kasar indiyawa da ‘yan filifin ne kuma yawanci ma’aikatan jinya da likitoci ne a kasar. A wannan lokacin sun samu damar sakata tare da walawa don yin bikin addininsu a sarari.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban kasar Gambia zai fuskanci fushin doka saboda kashe wasu 'yan Najeriya

The Islamic Information ta ruwaito cewa, hatta ‘yan kasar Saudiyyar sun ji dadin yadda aka yi bukukuwan kirsimeti. Iyalai da dama sun yi shagulgulan tare da ma’aikatansu a gidajensu.

Wata ma’aikaciya a Saudiyya, Hadoon, ta bayyana irin dadin da ta ji tare da iyalanta sakamakon shagalin da bikin kirsimeti tare da ma’aikaciyarsu kirista.

Sun yi shagalin tare da Ajigo, wacce Hatoon ta dauka tamkar ‘yar gida inda suka yi girke-girke na gani da fadi.

“Mun yi shagalin da daddare inda mu ka kawata wurin cin abincinmu da fulawoyi masu kaloli irin na kirsimeti a ranar sannan muka yi abinci na gani da fadi,” a cewar Hadoon.

Saboda dakatar da dokar hana shige da fice a kasar Saudiyya, Ajigo ta samu damar yin bikin kirsimeti tare da ‘yan uwanta.

“Yan kasar Saudi Arabia sun fahimci muhimmancin girmama addinan wasu da kuma yin shagulgula idan sun samu dama,” a cewar Ajigo.

Kara karanta wannan

Bayan shekaru 6, gwamnatin Katsina ta bayyana lokacin da za ayi zaben kansiloli

A Jeddah da sauran birane da ke Saudiyya, kasuwanni da gidajen biredi sun dinga kyautar kayan makulashe duk saboda shagalin kirsimetin.

A shekarun baya, an fara sayar da kayan kawata wurare na bikin kirsimeti a kasuwanni amma abin bai kai na wannan shekarar ba.

A baya samun bishiyar ado ta kirsimeti ba kankanin aiki bane amma a wannan shekarar har kyautar ta aka dinga yi sannan har sutturun yara da na manya duk an sayar dasu a shekarar nan masu dauke da ado irin na kirsimeti.

A kasuwannin kasar, safuna da rigunan sanyi da duk wasu abubuwan bukata sun yawaita, haka mutane suka dinga bayyana sanye da sutturu masu kalar jajaye, koraye da kuma farare.

A karon farko, an yi bikin Kirsimeti a kasar Saudi Arabiya a 2021
A karon farko, an yi bikin Kirsimeti a kasar Saudi Arabiya a 2021. Hoto daga saudigazette.com.sa
Asali: UGC

Asali: Legit.ng

Online view pixel