Gwamnatin Buhari na kitsa yadda za ta kashe ni, Sunday Igboho

Gwamnatin Buhari na kitsa yadda za ta kashe ni, Sunday Igboho

  • Mai rajin kafa kasar yarabawa, Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho ya zargi gwamnatin Najeriya da yunkurin batar da shi a jamhuriyar Benin
  • Dama tun ranar 19 ga watan Yulin da ya gabata hukuma ta kama shi a Kwatano duk da kokarin da aka dinga yi don sakin shi amma abin ya ci tura don ya kwashe fiye da kwanaki 161 a tsare
  • Kakakin Igboho, Olayomi Koiki, a ranar Talata ya saki bayani akan yadda gwamnatin tarayya take aiki da shugaban jamhuriyar Benin, Patrice Talon don maido da Igboho Najeriya

Jamhuriyar Benin - Mai fafutikan kafa kasar Yarbawa, Sunday Adeyemo, da aka fi sani da Sunday Igboho, ya yi zargin cewa Gwamnatin Tarayyar Najeriya na shirin halaka shi a kasar Jamhuriyar Nijar, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Akwai hannun Gwamnoni wajen kawowa Buhari matsalar tsaro inji Tsohon Shugaban Majalisa

Idan ba a manta ba jami’an tsaron Brigade Criminelle sun kama Igboho a ranar 19 ga watan Yulin a Kwatano. Duk da duk kokarin da aka yi don sakinsa abin ya ci tura don ya kwashe kwana 161 a hannunsu.

Gwamnatin Buhari na kitsa yadda za ta kashe ni, Sunday Igboho
Igboho ya ce gwamnatin Buhari na son halaka shi. Hoto: Vanguard NGR
Asali: Facebook

Olayomi Koiki, Kakakin Igboho, a wata murya da ya saki a ranar Talata da yamma, ya zargi shugaban kasa Patrice Talon na Jamhuriyar Benin da aiki da Gwamnatin Najeriya wurin ganin sun dawo da Igboho Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce ba za su samu nasarar halaka Igboho ba

A cewarsa:

“Mutane da dama sun ji jita-jita tsakanin sa’o’i 24 zuwa 48 akan lamarin. Mun san Ubangiji yana kallo.
“Idan su na kokarin yi ne to ba za su taba samun nasara ba. Su na shirin yin mugun abu akan Farfesa Banji Akintoye da sauransu, kawai su na kokari ne kawai amma Ubangiji ya fisu.

Kara karanta wannan

Sanata Shehu Sani ya gwangwanje jami'an kan hanya da kyautukan kirsimeti a Kaduna

“Makiya su na kokarin ganin bayansa (Igboho). Su na shirin ganin bayansa don a dakata da batun kafa kasar Yarabawa, amma Ubangiji ya nuna musu cewa ya fi su. Idan ku na tunanin shari’a za ta sakar mana shi, bata lokacin mu kawai muke yi.”

Jamhuriyar Benin ba za ta sake shi ba har sai shugaban kasa ya amince

Ya bayyana cewa shari’ar jamhuriyar Benin ba ta aiki saboda yadda su ke ta jan zaren da tsawo kamar yadda ya zo a rahoton na Vanguard.

A cewarsa ya yi magana da lauyoyi a Benin kuma sun fada masa cewa shugaban kasa ne kadai zai iya sakinsa.

Ya ce akwai bukatar su yi yaki don neman ‘yancin su. Ya misalta hakan da yadda su ka halaka MKO Abiola da Funsho Williams saboda zalunci.

Jami’an hukumar ‘yan sanda ta fararen kaya, DSS sun je har gidan Sunday Igboho a ranar 1 ga watan Yuli inda su ka je bincike bisa zarginsa da ajiye miyagun makamai.

Kara karanta wannan

Bincike ya bayyana asarar biliyoyi da gwamnati ta yi saboda dakatar da Twitter

Yadda aka birne Sarkin masu bautan Sheɗan na Najeriya a cikin mota tare da saka masa waƙar da yafi so

A wani labarin, Ganau sun tabbatar da yadda aka birne Sarkin Shaidanu, Simon Odo a mota wacce injin dinta ya ke kunne tare da wakar da ya fi so tana tashi, Sahara Reporters ta ruwaito.

An birne Simon Odo, wanda aka fi sani da Sarkin Shaidanu a cikin motarsa cikin kauyensu da ke kudu maso gabashin jihar Enugu bayan ya mutu ya na da shekaru 74, BBC News ta ruwaito.

Injin din motar a kunne ya ke sanda aka birne shi sannan an sa wakar da ya fi so a cikin motar, wanda hakan ne ya zama karo na farko da irin wannan lamari ya faru a kauyen Aji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel