Yadda aka birne Sarkin masu bautan Sheɗan na Najeriya a cikin mota tare da saka masa waƙar da yafi so

Yadda aka birne Sarkin masu bautan Sheɗan na Najeriya a cikin mota tare da saka masa waƙar da yafi so

  • Ganau sun tabbatar da yadda aka birne Sarkin Shaidanu, Simon Odo a cikin mota wacce aka yi amfani da ita a matsayin akwatin gawa
  • Lamarin ya faru ne a kauyensu da ke kudu maso gabashin jihar Enugu bayan ya mutu ya na da shekaru 74 a duniya
  • An bayyana yadda injin motar ya ke a kunne yayin da aka sa wakar da ya fi so tana tashi a cikin motar, lamarin da ba a taba yin irinsa ba

Jihar Enugu - Ganau sun tabbatar da yadda aka birne Sarkin Shaidanu, Simon Odo a mota wacce injin dinta ya ke kunne tare da wakar da ya fi so tana tashi, Sahara Reporters ta ruwaito.

An birne Simon Odo, wanda aka fi sani da Sarkin Shaidanu a cikin motarsa cikin kauyensu da ke kudu maso gabashin jihar Enugu bayan ya mutu ya na da shekaru 74, BBC News ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sarkin Sheɗanu: Fitaccen Mai Maganin Gargajiya Na Najeriya Mai Mata 59 Da ƳaƳa Fiye Da 300 Ya Mutu

Yadda aka birne Sarkin masu bautan Sheɗan na Najeriya cikin mota yayin da waƙar da yafi so take tashi
An birne Sarkin Shedanu, Simon Odo, a cikin mota tare da kuna masa wakar da ya fi so. Hoto: SaharaReporters
Asali: Facebook

Injin din motar a kunne ya ke sanda aka birne shi sannan an sa wakar da ya fi so a cikin motar, wanda hakan ne ya zama karo na farko da irin wannan lamari ya faru a kauyen Aji.

Shi ya yi wasiyya akan a birne shi haka

Mr Odo da kansa ya bukaci a birne shi a haka, kamar yadda dansa, Uchenna Odo ya sanar.

Wannan birniyar da aka yi masa tare da abin hawa na nuna irin sa’ar da yayi ta tafiya wata sabuwar duniya, a cewar wasu yaransa.

Odo ya auri mata sun kai 57.

Wasu daga cikin ‘yan uwansa sun shaida wa BBC Igbo yayin da wakilinsu ya kai ziyara kauyen Aji da safe, cewa mutum ne mai mutunci da mu’amala da mutane.

Kara karanta wannan

Bidiyon matashi mai bautar ƙasa ya na neman auren soja a sansanin NYSC ya ƙayatar

Da safiyar Talata ya rasu

Tun safiyar ranar Talata Odo ya rasu.

Yayin tattaunawa da BBC Igbo a 2020, Mr Odo ya shaida yadda ya gaji bautar shaidan daga iyaye da kakanninsa wadanda duk shi su ke bauta mawa.

A cewarsa ya na da mata 57 amma ya manta yawan yara da jikokinsa.

Matar Shahararren Tsohon Gwamnan Najeriya Ta Rasu a Asibiti a Amurka

A wani labarin, Njideka Ezeife, matar tsohon gwamnan jihar Anambra wanda kuma dattijo ne a kasa, Chief Chukwuemeka Ezeife ta riga mu gidan gaskiya.

Njieka ta rasu ne bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a wani asibiti da ke Amurka kamar yadda kungiyar dattawan Igbo ta sanar ta bakin sakatarenta Farfasa Charles Nwekeaku, The Sun ta ruwaito.

Nwekeaku ya ce ana sa ran tsohuwar matar gwamnan za ta dawo Najeriya ne a ranar Litinin, 13 ga watan Disamban 2021 amma kwatsam ta fara rashin lafiya.

Kara karanta wannan

Mutane 16 sun mutu a hatsarin mota a Bauchi, Hukumar FRSC

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel