Akwai hannun Gwamnoni wajen kawowa Buhari matsalar tsaro inji Tsohon Shugaban Majalisa

Akwai hannun Gwamnoni wajen kawowa Buhari matsalar tsaro inji Tsohon Shugaban Majalisa

  • Tsohon shugaban majalisar dattawa, Ameh Ebute ya koka a kan halin tsaro da ake ciki a Najeriya
  • Sanata Ameh Ebute yana ganin akwai hannun wasu masu mulki a cikin abubuwan da ke faruwa
  • A sakon kirmeti da ya fitar a makon da ya wuce, ‘Dan siyasar yace ana kokarin kawowa Buhari cikas

Benue - Tsohon shugaban majalisar dattawa na kasa, Ameh Ebute ya fito y ana zargin wasu gwamnoni da jawo matsalar rashin tsaro a jihohin Najeriya.

Jaridar The Sun tace a sakonsa na bikin kirismeti, Sanata Ameh Ebute ya koka a kan yadda wasu shugabanni suka zama masu taimakawa harkar ta’addanci.

Ameh Ebute ya yi wa wannan sako da ya fitar take da ‘The gathering storm must not consume US’, ya na gargadin cewa ka da wannan rigima ta ci kowa.

Kara karanta wannan

Bayan Hadiman Shugaban kasa sun kamu da COVID-19, an bayyana halin da Buhari ke ciki

Rahoton yace tsohon ‘dan siyasar ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a sha’anin shugabanci su dage wajen hada-kan al’umma, su guji abin da zai tarwatsa mutane.

Ebute ya tunawa al’umma cewa a lokacin zaben 2019, wasu ‘yan adawar siyasa da ke jam’iyya PDP sun yi alkawarin rusa kasar nan muddin suka fadi zabe.

Hafsun Sojoji
Shugaba Buhari da Hafsun Sojoji Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An yi alkawarin hana Buhari sakat - Ebute

“Ko dai wannan tsautsayi aka samu ko duk yakin neman zabe ne, tun da Buhari ya yi nasara a zaben gaskiyar da aka yi, ba a samu zaman lafiya a Najeriya ba.”
“Duk masu sa ido a harkar zabe daga kasashen ketare, har da Birtaniya, sun yabawa Najeriya a game da wannan zaben shugabannin da aka yi.” - Ameh Ebute.

A jawabinsa, Ameh Ebute yace gwamnonin da ke kan mulki su na da hannu a ta’adin da ake yi, sannan kuma ya yaba da irin kokarin da gwamnatin APC ke yi.

Kara karanta wannan

Muryar jami'in EFCC ya na sanar da yadda Malami ke kange masu cin rashawa ta bayyana

“Da rana Gwamnoni su na karyar ‘yan kishin kasa, cikin dare sai su zumbula rigar ‘yan ta’adda. Idan shugabanninmu za su yaudare mu, abin da takaici.”
Alamu sun nuna cewa shugaba Buhari ya fi sauran shugabannin Najeriya da aka yi a baya dagewa wajen shawo kan matsalar tsaron kasar nan.” - Ameh Ebute.

COVID-19 ta hargitsa Aso Villa

Fadar Shugaban kasa tayi bayani game da halin da Shugaba Muhammadu Buhari suke ciki a yanzu bayan jin su Malam Garba Shehu sun kamu da COVID-19.

Da yake bayani a ranar Lahadi, Femi Adesina yace dirar da cutar Coronavirus tayi wa fadar Aso Rock, ya nuna hadiman shugaban kasa mutane ne kamar kowa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel