Yanzu-Yanzu: Ƙanin Fitaccen Ɗan Kwallo Maradona Ya Mutu

Yanzu-Yanzu: Ƙanin Fitaccen Ɗan Kwallo Maradona Ya Mutu

  • Allah ya yi wa Hugo Maradona, kanin fitaccen dan kwallon duniya na Argentina, Diego Maradona rasuwa
  • Marigayi Hugo ya rasu ne misalin karfe 11.50 na safe a gidansa da ke birnin Naples sakamakon bugun zuciya
  • Hugo ya rasu ne yana da shekaru 52 a duniya, ya kuma bar matan aure daya, Paola Morra da 'ya'ya guda uku

Argentina - Hugo Maradona, kanin fitaccen dan kwallon duniya dan kasar Argentina, ya rasu sakamakon bugun zuciya yana da shekaru 52 a duniya, Daily Trust ta ruwaito.

Hugo ya rasu ne misalin karfe 11.50 na safe a gidansa da ke Naples, birnin da Diego Maradona ya buga wasar kwallo a lokacin da ya yi tashe sosai inda shima Hugo ya buga kwallo a matakin matasa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tashin hankali yayin da mota dauke da fasinjojinta ta fada magudanar ruwa

Yanzu-Yanzu: Ƙanin Fitaccen Ɗan Kwallo Maradona Ya Mutu
Hugo Maradona, Ƙanin Fitaccen Ɗan Kwallo Diego Maradona Ya Mutu. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Hakan na zuwa ne watanni 13 bayan bugun zuciyar ta yi sanadin rasuwar Diego - Jarumin Argentina da ya taya ta cin kofin duniya kuma daya daga cikin jaruman kwallon kafa a duniya, wanda ya mutu a Nuwamban 2020 yana da shekaru 60.

An ga Hugo a filin motsa jiki na Maradona da ke Naples wurin wani taro da aka shirya don karrama yayansa wata guda da ta gabata, rahoton Daily Trust.

Ya rasu ya bar matarsa Paola Morra wanda ya aura a 2016 da yaransu uku.

Kungiyar Napoli ta tabbatar da rasuwar Hugo

Kungiyar Napoli ta tabbatar da rasuwar Hugo a wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Intanet tana mai cewa ya mutu ne sakamakon bugun zuciya.

Shugaban kungiyar Napoli, Aurelio De Laurentiis da kungiyar suna tarayya da iyalan Maradona wurin jimamin rashin Hugo.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Katafaren kantin 'Next Cash and Carry' da ke Abuja ya na ci da wuta

Kasashen da Hugo ya buga kwallo

Hugo Maradona ya buga kwallo a Italy, Austria, Spain, Argentina da Japan kafin ya koma Italy dindindin ya fara aikin kocin kananan kungiyoyi a Naples.

Maradona ya shiga siyasa inda ya yi takara amma bai yi nasara ba.

Kungiyar Napoli ta siya Hugo Maradona a shekarar 1987 - inda ya tarar da yayansa Diego - kafin daga bisani a bada aronsa ga kungiyar Ascoli.

A ranar 20 ga watan Satumbar shekarar 1987, yan uwan biyun sun yi karo da juna amma bangaren su Diego ne suka yi nasara da 2-1.

Ronaldinho da shahararrun ‘Yan wasan kwallon kafa 6 da suka tsiyace bayan sun yi ritaya

Wasan kwallon kafa yana kawo kudi mai yawan gaske. Baya ga shahara da suna da ‘dan wasa zai yi

Sai dai kuma babu tabbacin za a mutu a haka, ‘yan wasa da-dama sun tsiyace da suka daina buga kwallo

Kara karanta wannan

Babban Magana: 'Yan Ta'adda Dagar Kasar Waje Na Shirin Kai Hari a Abuja

Duk da irin makudan kudin da wadannan shahararrun taurari su ka tara, yanzu ba su da komai a rayuwa

Asali: Legit.ng

Online view pixel